Hukumar JAMB zata sake gudanar da jarabawan ga wasu dalibai

Hukumar JAMB zata sake gudanar da jarabawan ga wasu dalibai

Akalla dalibai 62,140 ne zasu sake rubuta jarabawa shiga makarantun gaba da sakandare wato JAMB na bana.

Shugaban hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede, yayi bayani a wata hira da manema labarai ranan Laraba cewa an shirya ranan 1 ga watan Yuli domin rubuta wani jarabawan.

Kana hukumar JAMB ta sallami wajajen rubuta jarabawa 24 bisa abubuwan da suka shafi kayan aiki.

Sakamakon dalibai 62,140 da aka watsar ya kunshi 57,646 da ake zargi da satan amsa, 3,811 rashin rijista da wuri, da kuma 683 wadanda aka samu matsalan hoto.

Amma hukumar tayi watsi da sakamakon dalibai 2,052 da ake da yakinin sunyi satar amsa.

Mun baiwa dalibai 62,140 daman sake rubuta jarabawan JAMB ranan 1 ga Yuli – Shugaban JAMB, Ishaq Oloyede

Mun baiwa dalibai 62,140 daman sake rubuta jarabawan JAMB ranan 1 ga Yuli – Shugaban JAMB, Ishaq Oloyede

Yayi bayanin cewa daliban da ake baiwa daman sake rubuta an basu ne domin anyi satar amsa a wuraren da suka rubuta amma babu yakinin cewa kowannensu yayi satar.

KU KARANTA: An zuba zaratan yan sanda 600 hanyar Kaduna zuwa Abuja

JAMB ta jaddada cewa dalibai 1,722,236 ne sukayi rijisan jarabawan bana wanda shine adadin mafi yawa a tarihin jarabawar.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel