Inyamurai su bar Arewa kawai, matasan Arewa zasu kai musu mamaya – Cif Ekene Enefe

Inyamurai su bar Arewa kawai, matasan Arewa zasu kai musu mamaya – Cif Ekene Enefe

Wani babban jigon jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) a jihar Anambra, Chief Ekene Enefe, ya gargadi yan kabilar Igbo su dawo gida kawai.

Enefe ya baiwa Igbo shawaran kada su saki jiki su cigaba da zama a Arewa saboda kada a kai musu mamaya, ya kara da wata Karin magana inda yace “Ai ba’a fadawa kurma an fara yaki”.

Cif Enefe yayi mamakin cewa shin meyasa har yanzu ba’a kama wadanda sukayi wannan magana ba. Kana wasu dattawan Arewa sun goyi bayan maganan matasansu.

Shin ta wani dalili zakace Igbo su kwantar da hankulansu tunda har yanzu ba’a kama ko mutum daya cikin matasan arewan da sukayi magana mai iya tada kura ba, ba cewa Igbo su bar yankinu.”

Inyamurai su bar Arewa kawai, matasan Arewa zasu kai musu mamaya – Cif Ekene Enefe

Inyamurai su bar Arewa kawai, matasan Arewa zasu kai musu mamaya – Cif Ekene Enefe

“Gwamnatin tarayya bata gaskiya cikin al’amarin nan. ya kamata ace an daure wadanda sukayi wannan magana idan basu wani rufa-rufa cikin al’amarin.”

“Wanna a shi bane karo na farko da Igbo ke fuskantan irin wannan matsala ba. Idan ba juya mukaddashin shugaban kasa yan Arewa keyi ba, to ya bada umurnin damke matasan Arewa.”

KU KARANTA: Shin Buhari zai iya karashe wa'adin mulkinsa har ya zarce?

“Ladabtar da su zai zama izina kuma ya kwantarwa Igbo hankali domin su cigaba da zama a yankin saboda za’a tsare su.”

A ranan Laraba, mukaddashin shugaban kasa ya gana da shugabannin Arewa inda yace musu ba zai amince da irin wadannan magnganu ba.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An bukaci Buhari ya yiwa Obasanjo, 'Yar'adua, Jonathan binciken kwa-kwaf

An bukaci Buhari ya yiwa Obasanjo, 'Yar'adua, Jonathan binciken kwa-kwaf

Kungiya ta bukaci Buhari ya yiwa gwamnatocin bayan sa binciken kwa-kwaf
NAIJ.com
Mailfire view pixel