An sake sace wani babba a gwamnati don neman fansa

An sake sace wani babba a gwamnati don neman fansa

- Ehimoni na hanyarsa ta Ondo domin dauko 'yan makaranta

- An bukaci iyalinsa su turo miliyan arba'in

A yayin da gwamnati ke cewa tana kokarin shawo kan matsalar satar mutane, sai gashi a yau ma an sake sace wani tsohon hadimin kakain majalisar jihar Kogi, a hanyarsa ta zuwa dauko iyalansa daga makaranta a jihar Ondo.

An dai yo wayar tarho daga inda ake boye dashi, an kuma bukaci da su biya naira miliyan 40 kafin a sako musu shi da ransa. Makudan kudin da iyalan suka ce bassu da shi.

KU KARANTA KUMA: Abin kunya: Saudi ta aikowa Najeriya dabino sadaka amma an saidaAbin kunya: Saudi ta aikowa Najeriya dabino sadaka amma an saida

Amma hukumar 'yan sanda tace har zuwa yanzu bata ma san da lamarin a hukumance ba.

David Ehimoni dai ya bar gwamnati, kuma dan kasuwa ne mai zaman kansa, wanda a yanzu haka ba'a san inda suka kaishi ba.

Ku biyo mu don jin yadda ceton wannan tahikin zata kaya...

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duba da sakamakon babban zaben PDP, anya Atiku bai yi kamun gafiyar baidu ba?

Duba da sakamakon babban zaben PDP, anya Atiku bai yi kamun gafiyar baidu ba?

Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi
NAIJ.com
Mailfire view pixel