Hukumar kwastan ta kama kayan fasa kwauri

Hukumar kwastan ta kama kayan fasa kwauri

- Hukumar kwastan shiyar jihohin Legas da Ogun ta kama kayan fasa kwauri na miliyoyin naira

- Hukumar ta bayyana cewa akasarin kayayyakin da ta kama , kayayyaki ne da suka hada da shinkafa da tayoyin mota

- Shugaban hukumar Kwastan mai kula da shiya ta 1 ya ce adadin farashin kayan da suka kama ya kai naira miliyan 608.7.

Hukumar kwastan mai kula da shiya ta 1, data kunshi jihohin Legas da Ogun ta kama kayan fasa kwauri na miliyoyin naira cikin kasa da watani biyu.

Shugaban hukumar Kwastan mai kula da shiya ta 1, Kwanturola Mohammed Uba Garba ne ya sanar da haka a wani taron manema labrai da ya kira a birnin Lagos.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, kwanturolan ya bayyana cewa akasarin kayayyakin da hukumar ta kama, kayayyaki ne da suka hada da shinkafa da tayoyin mota da ake kira “tokumbo”, da kuma wadansu kayayyaki da aka hana shigowa da su, ko kuma kayayyakin da aka bada izinin shigowa dasu, amma aka yi amfani dasu wajen boye kayayyakin da aka hana shigowa da su.

Hukumar kwastan ta kama kayan fasa kwauri

Kayayyakin fasa kwauri da hukumar kwastan ta kama

Ya bayyana cewa, sun kama shinkafa buhu 6,356, wanda darajar kudinsa shine naira miliyan 78.3. Ya kuma ce, hukumar ta kama ganyen wiwi kunshi 384 wanda yace an kimanta cewa kudinshi zai iya kaiwa naira miliyan 18.4.

KU KARANTA: Sanata Dino bai samu tarbiyya na kwarai daga gida ba – Gwamna Yahaya Bello

Yace akwai kuma tayoyi da aka hana shigowa dasu 4,984u, wanda su kansu adadin kudinsu ya kai miliyan 42. Akwai kuma motoci guda 12 wadanda kudinsu ya kai miliyan 58.8.

Kwanturola Mohammed Uba Garba ya bayyana cewa, adadin farashin kayan da suka kama ya kai naira miliyan 608.7.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Farashin kayayyaki a kasuwa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras

Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras

Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras
NAIJ.com
Mailfire view pixel