Sanata Dino bai samu tarbiyya na kwarai daga gida ba – Gwamna Yahaya Bello

Sanata Dino bai samu tarbiyya na kwarai daga gida ba – Gwamna Yahaya Bello

- Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce rashin samun cikakken tarbiyya da ya dace ne ke sa sanata Dino Melaye yin abin da ya ga dama

- Wannan ya biyo bayan kira da Dino ya yi na kalubalantan gwamnan da ya fito ya bada bayanai akan yadda yake kashe kudaden jihar

- Haka zalika a ranar Laraba Dino ya yi ma gwamnan tatas a majalisa inda yace gwamnan bai san abinda ya keyi ba

Wutar kiyayyan da ke tsakanin Sanata mai wakiltan Kogi ta Yamma Sanata Dino Melaye da Gwamnan jihar Yahaya Bello na ci gaba da ruruwa.

Bayan zargin gwamna Yahaya Bello da sanata Dino ya yi na cewa shine ya aika wasu bata gari domin su kashe shi a wani hari da aka kai masa lokacin da yake gudanar da wata zanga-zanga a jihar, ya kuma kalubalanci gwamnan da ya fito ya bada bayanai akan yadda yake kashe kudaden jihar.

KU KARANTA KUMA: Abin kunya: Saudi ta aikowa Najeriya dabino sadaka amma an saida

Sanata Dino bai samu tarbiyya na kwarai daga gida ba – Gwamna Yahaya Bello

Sanata Dino bai samu tarbiyya na kwarai daga gida ba inji Gwamna Yahaya Bello

Da yake zantawa da manema labarai a Abuja, gwamnan Yahaya Bello ya ce rashin samun cikakken tarbiyya da ya dace ne ke sa sanatan yin abin da ya ga dama.

“ Idan mutum bai sami tarbiyya na kwarai ba zaka ga ya zama fitina ga al’umma. Idan kuma al’umma suka kasa canza shi sai kaga ya gagare su. Daga nan ne fa dole sai gwamnati ta sa hannu wajen seta shi."

Ko da yake shima Sanata Dino ba kanwan lasa bane domin yayi wa Yayaha Bello tatas a majalisa ranar Laraba inda yace gwamnan bai san abinda ya keyi ba kuma ya roki majalisar da ta kafa dokar ta baci a jihar.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

NAIJ.com ta kawo maku bidiyo na sharhi a kan ko sabon Jam'iyya za su kawo karshen matsalolin siyasar Najeriya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiya ta bukaci Buhari ya yiwa gwamnatocin bayan sa binciken kwa-kwaf

Kungiya ta bukaci Buhari ya yiwa gwamnatocin bayan sa binciken kwa-kwaf

Kungiya ta bukaci Buhari ya yiwa gwamnatocin bayan sa binciken kwa-kwaf
NAIJ.com
Mailfire view pixel