Muna cikin kunci da bakin ciki a yankin Igbo – Inji wasu ‘yan Arewa

Muna cikin kunci da bakin ciki a yankin Igbo – Inji wasu ‘yan Arewa

- Wasu ‘yan arewa sun ce suna rayuwa cikin kunci da bakin ciki saboda yawan tsangwamarsu da ake yi a jihohin kabilar Igbo

- Kabilar Igbo mazauna yankin arewa suna zaune a yankin arewa suna yin walwala suna yin komai

- Wasu ‘yan arewa mazauna jihohin kabilar Igbo sun ce basu ga laifin abin da matasan arewar suka yi ba

Wani dan arewa mazaunin yankin al'ummar Igbo ya ce suna rayuwa cikin kunci da bakin ciki saboda yawan tsangwamarsu da ake yi a jihohin kabilar Igbo a Najeriya.

Ya ce abin da wasu matasan arewa suka yi na ba wa 'yan kabilar igbo wa'adin wata uku don su bar yankin ya yi daidai kuma muna goyon bayansu matuka gaya.

A cewarsa su mutanensu (kabilar Igbo) suna zaune a yankin arewa suna yin walwala suna yin komai, kuma ana kula da su duk wasu hakkoƙi ana kare musu, amma mu ba haka abin yake ba a nan.

Kamar yadda NAIJ.com ta samu daga shafin, Alhaji Haruna Sulaiman Wudil, wanda ya shafe kimanin shekara 40 yana zaune a birnin kasuwanci na Anaca a jihar Anambra, ya ce shi kam bai ga laifin abin da matasan arewar suka yi ba.

Ya ce duk illar da wa'adin da aka ba Igbo a arewa zai kawo, sun ga takurar da ta fi haka a yankin kudu maso gabas.

A cewarsa duk abin da suke yi a can suna cikin taka-tsantsan a tsorace.

Ana nuna fargabar cewa matuƙar kiran ya yi tasiri har 'yan ƙabilar Igbo suka fara komawa yankinsu, hakan zai tilasta wa su ma mutanen yankin arewa da ke kudu maso gabas barin yankin, abin da ka iya ta'azzara rarrabuwar kai.

Shi ma, Alhaji Abdullahi Illela, wani ɗan arewa da ya kwashe aƙalla shekara 25 a garin Nnewi na jihar ta Anambra, ya ce babu abin da zai dame su idan aka ce su tashi su koma yankinsu, don kuwa ba su ajiye koma a can ba.

Ya ce muna nan muna neman abinci a cikinsu, amma saboda yawan tashin hankalinsu kullum muna cikin fargaba.

"Yadda 'yan arewa suka yi, gaskiya sun yi daidai," in ji Alhaji Illela.

KU KARANTA: Korar Inyamurai: Matasan arewa sun dauka ta da zafi – inji Rochas

Ya ce a can (yankin arewa) suna rayuwarsu ba tare da wata tsangwama ba, babu wani tashin hankali amma mu nan da zarar ka yi magana sai su ce ai ba ƙasarku ce ba.

A cewarsa ko masallacin Juma'a ba su da shi a garin Nnewi:"inda muke sallah haya muke yi wallahi."

Tuni dai hukumomi da wasu manyan jami'an gwamnati suka yi Allah wadai da irin waɗannan kiraye-kiraye na cewa wasu su tashi daga wani yanki su koma jihohinsu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shekaru 50 da fara fafutukar kafa kasar Biyafara, shin 'yan kabilar Igbo za su iya cimma burinsu kuwa?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel