Gwamna Geidam: Ba wanda zai tsangwami kabilar Ibo a kan ido na

Gwamna Geidam: Ba wanda zai tsangwami kabilar Ibo a kan ido na

- Gwamna Geidan ya sha alwashin kare kabilun jiharsa

- An baiwa kabilun ibo wa'adin watanni uku su bar arewa a baya

- An sami cece-kuce tsakanin kabilun Arewa da na Kudu

Gwamnan jihar yobe, wadda ke farfadowa daga tashin hankalin Boko haram shekaru da yawa, ya sha alwashin kare kabilun Ibo da ke jiharsa, inda yace babu wanda zai tsangwame su, babu kuma mai korar su ko uzzura musu, wannan na zuwa ne lokacin da ake yamadidin cewa sai kabilun sun bar arewa.

Hadimin gwamnan Abdullahi Bego, shine ya fitar da sanarwar, da yawun gwamnan jihar, inda yace akwai kabilar Ibo dai sune cikin kowacce karamar hukuma 17 dake cikin jihar, ya kuma ce gwamnatinsu na maraba da kowa, yayi walwalarsa ya kuma nemi arziki.

KU KARANTA KUMA: Abin kunya: Saudi ta aikowa Najeriya dabino sadaka amma an saida

Gwamna Geidam: 'Ba wanda zai tsangwami kabilar Ibo a kan ido na'

Gwamna Geidam: 'Ba wanda zai tsangwami kabilar Ibo a kan ido na'

"Mu a nan a jihar Yobe, tun fil-azal, kabilun kasar nan da ma na wasu kasashen, suna zaman lafiya da juna tun tali-tali, ba wani tsoro ko tsangwama, babu wanda ya ke cin zarafin wani, toh hakan ne zamu ci gaba da dabbakawa", Sanarwar ta ce.

A dai baya-bayan nan wasu samari 'yan ta kife da ma wasu da suke kiran kansu dattijai a yankin arewa, na cikin masu kiraye kiraye na cewa wai sai kabilun ibo sun bar yankin.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Jam'iyya za su kawo karshen matsalolin siyasar Najeriya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel