Hamshakin mai kudi da aka gano ashe mutane yake sacewa ya bada sunayen wadanda 'ya sha jininsu'

Hamshakin mai kudi da aka gano ashe mutane yake sacewa ya bada sunayen wadanda 'ya sha jininsu'

- Bayan da aka cewa wani hamshakin mai-kudi shine ke haddasa mafi yawan sacewa da garkuwa da jama'a a birnin lagos da kewaye

- An sami makamai da yawa da kudi na kasashe daban daban

- A cewarsa, aikin shedan ne, a yafe masa, duka da cewa hukuncin kisa ne a jihar Legas ayi garkuwa da mutum

A jihar Legas, bayan kama hamshakin dan sace mutane ayi garkuwa dasu, Mr Evans, ya ce ya tuba, a yafe masa, ya kuma ce shi da wasu mata iyalinsa ne da suke taimaka masa, ya bada sunayen wadanda ya sace da kudin da aka biyashi na fansar su.

KU KARANTA KUMA: Abin kunya: Saudi ta aikowa Najeriya dabino sadaka amma an saida

Hamshakin mai kudi da aka gano ashe mutane yake sacewa ya bada sunayen wadanda 'ya sha jininsu'

Hamshakin mai kudi da aka gano ashe mutane yake sacewa ya bada sunayen wadanda 'ya sha jininsu'

1. Mbarikatta William Uboma, a 2012, an biya Naira miliyan ashirin kafin su sako shi

2. Mista Paul Cole, shima haka aka biya Naira miliyan 20 a 2012

3. Mista Muhammed Jamal a 2012, shima miliyan 17 na naira.

4. Mista Kingsley a 2012, shima miliyan 15

5. Mista Anthony shima 15 na miliyoyi.

6. Mista Leo, shima miliyan sha biyar

7. Mista Randeki miliyan talatin N30m

8. Shugaban kamfanin Kings Paint naira miliyan 40

9. Wani da ba suna, dala miliyan 1, kusan Naira miliyan dari uku

10. Shugaban Uyi Technical, sai da ya biya naira miliyan 100, sannan suka sake shi.

Daga dai watan Janairu an zartas da dokar kashe wanda aka kama da laifin sata da garkuwa da mutane, amma shi wannan ja'irin yace a yanzu ya mika wa Yesu rayuwarsa, don haka ayi masa hakuri a yafe masa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiya ta bukaci Buhari ya yiwa gwamnatocin bayan sa binciken kwa-kwaf

Kungiya ta bukaci Buhari ya yiwa gwamnatocin bayan sa binciken kwa-kwaf

Kungiya ta bukaci Buhari ya yiwa gwamnatocin bayan sa binciken kwa-kwaf
NAIJ.com
Mailfire view pixel