Tsohon dan majalisa a Ingila yace mutanen Najeriya suna sakaci da batun lafiyar Buhari

Tsohon dan majalisa a Ingila yace mutanen Najeriya suna sakaci da batun lafiyar Buhari

- Tsohon dan majalisar Ingila, yace saboda sakacin mutan Najeriya, shugaba Buhari na iya mutuwa amma a ninke su aki gaya musu yadda batun yake

- Ana dai jinyar Buhari a Ingila, amma ba wani wanda ya ga shugaban kasar har yanzu

- Babu ranar da aka saka cewa shugaba Buhari zai dawo

Tsohon dan majalisar Ingila Eric Joyce, wanda yace hukumomin Najeriya sun rena talakawansu kan kin bayyana wa jama'a asalin bayani kan rashin lafiyar shugaba Buhari, ya ce cikin makonnin da aka shafe ba'a ga shugaba Buhari ba, tana iya yiwuwa ma ya mutu ne amma aka boye wa 'yan Najeriya.

Eric Stuart Joyce ya ma ce shugaba Buhari ya mutu tun tuni, amma wai an ki a gaya wa mutanen Najeriya gaskiya ne, saboda raina talakawa da gwamnatin tayi.

KU KARANTA KUMA: Masu rura wutar rikici za su fuskanci fushin hukuma — Osinbajo

Tsohon Dan Majalisa a Ingila yace mutanen Najeriya suna sakaci da batun lafiyar Buhari

Tsohon Dan Majalisa a Ingila yace mutanen Najeriya suna sakaci da batun lafiyar Buhari

A cewarsa, muddin ba'a fito an wa talakawa bayanin ko ina shugaban yake ba, talakawa ya kamata su yi bore su nemi jin bahasi.

"Idan wannan shugaban ya mutu, ya zama mutum na uku daga arewa da ya mutu a kan karagar mulki, amma wani daga kudu ya gaje shi."

Ya kuma yaba da hazakar mukaddashin shugaba Osinbajo inda ya ce yana da zafin nama da iya aiki, wanda zai iya zama cikakken shugaba idan aka bashi cikakkiyar dama.

Eric Joyce dai ya zama bature daya tilo da ya sanya ido sosai kan yadda gwamnatin Najeriya ke tafiya.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel