Sarki Sanusi ya bayyana asalin matsalar dake damun Najeriya

Sarki Sanusi ya bayyana asalin matsalar dake damun Najeriya

- A baya dai Sarki Sanusi ya yamutsa hazo kan batun siyasa da tattalin arziki

- Sarki Sanusi ya yi sabon tsokaci kan matsalar da Najeriya ke fuskanta

- Sarki Sanusi ya yi Allah-wadai da masu yada tsana a al'umma

A tsokacin sa na baya-bayan nan, mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, ya ayyana matsalar kabilanci da bangaranci a matsayin babbar matsala da ka iya hadiye kasar nan baki daya. Sarkin ya yi tir da Alla-wadai da masu ingiza rikici da tsana ta kabilanci a tsakanin kabilun kasar nan.

"Dole mu bar bin abin da iyaye da kakanni suka fadi a zamanisu, na kin juna da kabilanci da bangaranci, idan a 1953 Sir Olaniwon yayi wata maganar kabilanci baro-baro, baya nufin muma na wannan lokaci sai munyi koyi da wannan", Sarkin ya wallafa a shafinsa na Instagram.

KU KARANTA KUMA: Masu rura wutar rikici za su fuskanci fushin hukuma — Osinbajo

Da alama dai Sarkin na bayani ne kan irin rarrabuwar kai da kabilanci hade da bangaranci da aka yi ta samu a lokutan mulkin mallaka da ma bayan samun 'yancin kai, tsakanin manyar kasa, inda zaka ji mutum kamar Ahmadu Bello na fitar da kishinsa karara ga arewa, da nuna tsagwaron wariya ga wasu kabilun kasar nan.

Sarki Sanusi a bayyana asalin matsalar dake damun Najeriya

Sarki Sanusi a bayyana asalin matsalar dake damun Najeriya

Sarkin ya kara da cewa, ko kafin jihadin dan Fodio, kafin ma zuwan turawa, Hausawa na kashe kawunansu a cikin arewa, garuruwa irin su Zazzau, Kano da Hadejia na yakar junansu, zamani yayi da za'a dubi abin aga lokacin ya wuce, a rungumi juna a zauna tare a matsayin 'yan Najeriya, a cewarsa.

Sarkin ya kara da cewa: "In ka duba zaka ga ana cewa Babagida ya lalata tattalin arzikin kasa, ba'a la'akari da su waye suke cikin gwamnatinsa a lokacin, sai kaji ana cewa wai anyi murdiya a zabe, amma ai ko Obasanjo da Maurice Iwu sunyi murdiya a 2007."

Sarkin ya kuma yi tsokaci kan shugabanci, inda ya ce tun lokacin su Awolowo, ya zuwa yanzu, babu wani shugaba da ya kai irin kwazon iya mulkinsu, sai ma sata da wawaso tsakanin 'yan siyasa. Ya kara da cewa kuma satar batta da kabila, kowa ma yi yake.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel