Masu rura wutar rikici za su fuskanci fushin hukuma — Osinbajo

Masu rura wutar rikici za su fuskanci fushin hukuma — Osinbajo

- Mukaddashin shugaban kasa ya ce gwamnati zata dauki mataki a kan masu maganganun batanci da ka iya haddasa rikici a kasar

- Osinbajo na magana ne a kan wa'adin da wasu kungiyoyin Arewa suka diba ma 'yan kabilar Igbo

- Ya na ci gaba da tattaunawa da shugabanni daga bangarorin biyu

Mukaddashin shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa gwamnatin su ba zata zuba ido ta bari kungiyoyi ko wasu mutane na yin maganganun da zai iya tada zaune tsaye a kowani bangare na kasar nan ba.

Osinbajo ya fadi hakan ne da yake ganawa da shugabannin dattawan Arewa da suka kai masa ziyara a fadar shugaban kasa.

Ya kara da cewa dole gwamnati ta kara tsaurara matakai akan hakan domin gujewa barkewar rikicin da ba a shirya masa ba.

KU KARANTA KUMA: Abin kunya: Saudi ta aikowa Najeriya dabino sadaka amma an saida

“Yanzu da zarar rikici ta barke kawo karshen ta sai Allah kuma na sani cikin ku babu wanda yake so ace wai hakan ya faru ko da kuwa ace da makiyinsa ne.

“Ina kira ga dukkan ‘Yan Najeriya da mu zo mu hada kai da fata domin ganin mun kai kasarmu gaba duk da banbance-banbancen kabila da asali da muke dashi.”

Ya umurci dattawan arewan da su isar da wannan sako ga ‘yan Arewa.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli wannan bidiyo na NAIJ.com TV da ke tambaya kan ko mutun zai iya aure daga wata kabila daban da nasa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel