Wata sabuwa: Mahauta da dillalan shanu na yajin aiki a jihar Taraba

Wata sabuwa: Mahauta da dillalan shanu na yajin aiki a jihar Taraba

- An dade ana kai komo tsakanin gwamnati da makiyaya da manoma a jihar Taraba lamarin da ya kai ga gwamnatin gabatar da dokar hana kiwo a fili cikin jihar abun da Fulani kuma suka lashi takobin.

- Yanzu haka dai wannan yajin aikin da mahauta da kuma dillalan shanu dana dabbobi suka fada a jihar Taraban ya jefa jama’ar jihar cikin wani mawuyacin hali na rashin samun nama,inda kuma aka rufe kasuwannin dabbobi dake kawo wa jihar kudaden shiga .

NAIJ.com ta samu labarin cewa yajin aikin dai ya taso ne biyo bayan zanga-zangar lumanan da aka gudanar a majalisar dokokin jihar game da dokar hana kiwo a fili da gwamnan jihar ya kai gaban yan majalisar dokar da Fulani makiyaya ke cewa ba zata sabu ba,wai bindiga a ruwa!

Alhaji Umaru Usman da ake yiwa lakabi da Umaru-Jo,wanda shine ma shugaban kungiyar dillalan kananan dabbobi a jihar yace tun farko wannan mataki da gwamnan jihar ke son dauka na kafa dokar hana kiwo bata dace ba.

Wata sabuwa: Mahauta da dillalan shanu na yajin aiki a jihar Taraba

Wata sabuwa: Mahauta da dillalan shanu na yajin aiki a jihar Taraba

Da alamun dai wannan dambarwa ta jihar Taraban na neman shafan sauran jihohin arewa maso gabas. Umar Mafindi Danburam dake zama shugaban kungiyar Fulani ta Miyetti Allah shiyar arewa maso gabas ya bayyana matakin da suke son dauka.

Gwamnatin jihar dai ta fitar da wata sanarwa dauke da sa hannun hadimin gwamnan jihar ta fuskacin harkokin yada labarai Mr Sylvanus Giwa inda tayi tir da wannan yajin aikin da kawo yanzu ya kawo tsaiko a jihar.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiya ta bukaci Buhari ya yiwa gwamnatocin bayan sa binciken kwa-kwaf

Kungiya ta bukaci Buhari ya yiwa gwamnatocin bayan sa binciken kwa-kwaf

Kungiya ta bukaci Buhari ya yiwa gwamnatocin bayan sa binciken kwa-kwaf
NAIJ.com
Mailfire view pixel