Korar Inyamurai: Matasan arewa sun dauka ta da zafi – inji Rochas

Korar Inyamurai: Matasan arewa sun dauka ta da zafi – inji Rochas

- Gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha ya kalubalanci kungiyoyin IPOB, MASSOB, da kuma ta matasan Arewa kan kalaman da sukeyi na tunzura jama’a da kuma kawo rabuwar kai.

- Da yakewa manema labarai jawabi a gidan gwamnati dake Owerri, Okorocha ya musalta rahotannin da wasu kafafen yada labarai suka bayar cewa al’ummar yankin kudu maso gabas sun goyi bayan umarnin zaman gida da kungiyoyin fafutukar tabbatar da kasar Biafra suka bayar.

NAIJ.com ta samu labarin cewa da yake nisanta al’ummar kabilar Igbo daga fafutukar ta MASSOB da IPOB suke yi,gwamnan yakoka da kalaman matasan arewa inda yace kalaman sun fito ne daga bakin mutanen da basu san yaki ba.

Okorocha yace kalaman da suka fito daga bangarorin biyu, kalamai ne da kan iya haddasa yaki.

” Ina son na gargadi wadannan kungiyoyi da suke bukatar goyon baya da su daina da gaggawa saboda yaudara ce,” yace.

Korar Inyamurai: Matasan arewa sun dauka ta da zafi – inji Rochas

Korar Inyamurai: Matasan arewa sun dauka ta da zafi – inji Rochas

Amma kuma ya bayyana kabilar Igbo a matsayin masu son zaman lafiya da suke shiga kowanne bangare na kasarnan domin gudanar da harkokin kasuwancin su da kuma gina abota tare da sauran al’ummar kasa.

A cewarsa, Igbo ba kawai sun habaka birnin Legas da kuma sauran manyan biranen kasarnan bane, sunfi kuma kowa zuba jari a kasarnan.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC
NAIJ.com
Mailfire view pixel