Yaki da rashawa: ‘Yan Najeriya sun yi tir da nasarar Saraki ya samu a kotu

Yaki da rashawa: ‘Yan Najeriya sun yi tir da nasarar Saraki ya samu a kotu

- A jiya Laraba ne kotu ta wanke shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki a shari’ar da yake fuskanta akan laifin kin bayyana gaskiyar adadin kadaroroin da ya mallaka.

- Alkalin Kotun, Dan Ladi Umar ya ce masu karar sun gaza kawo shedun da za su tabbatar da cewa Saraki ya aikata laifin da ake tuhumarsa da shi.

Ga dukkan alamu dai wannan lamari bai yi wa ‘yan Nijeriya da yawa dadi ba, inda suka fito kwansu da kwarwatar su a shafukan sada zumunta suka nuna haka.

Yayin da wasu suka yi watsi da yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatin Buhari ta ce ta na yi, wasu kuwa dora laifin suka yi akan kotun, inda a nan ne aka wanke Bola Tinubu a lokacin da aka tuhume shi da irin wannan laifin.

Yaki da rashawa: ‘Yan Najeriya sun yi tir da nasarar Saraki ya samu a kotu

Yaki da rashawa: ‘Yan Najeriya sun yi tir da nasarar Saraki ya samu a kotu

NAIJ.com ta samu labarin cewa wasu kuwa haka suka ce gwara gwamnati ta manta da wannan yaki da cin hancin, ta mayar da hankali wajen farfado da tattalin arziki.

Wasu kuwa haka suka ce dama can tun lokacin da aka shigar da karar, sun san cewa ungula da kan zabo ce.

Wani Rahoto da jaridar Sahara Reporters ta wallafa ya kara jagula lamarin, inda ta nuna cewa Saraki ya biya alkalin kotun cin hancin dala miliyan biyu kafin ya yi watsi da karar.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel