Ku kara hakuri yan Najeriya, gwamnatin APC ba zata baku kunya ba - John Onyegun

Ku kara hakuri yan Najeriya, gwamnatin APC ba zata baku kunya ba - John Onyegun

- Shugaban jam’iyyar APC na kasa, John Odigie Oyegun, a wani zama na musamman da ‘yan jarida ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ba za ta ba ‘yan Najeriya kunya ba, wajen yin aikin azo a gani.

- Oyegun, ya fadi hakan ne a lokacin da babban mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yaki da cin hanci da rashawa Okoi Obono Obla, ya kai masa ziyara a Abuja.

Ya ce jam’iyyar APC na da masaniyar cewa a shirye ‘yan Najeriya suke su ki zaben ta matukar bata taka rawar gani ba kafin shekara ta 2019.

NAIJ.com ta samu labarin cewa sannan ya bukaci ‘yan ‘yan jam’iyyar da su ci gaba da bada gudunmawarsu dan ganin jam’iyyar ta taka rawar gani wajen yiwa al’umma aiki kafin zaben shekara ta 2019.

Ku kara hakuri yan Najeriya, gwamnatin APC ba zata baku kunya ba - John Onyegun

Ku kara hakuri yan Najeriya, gwamnatin APC ba zata baku kunya ba - John Onyegun

Sannan ya kara da cewa jam’iyyar za ta ci gaba da karban korafe-korafe, tare da yin gyararraki a dukkanin wuraren da ta yi kuskure, domin ci gaba da samun karbuwa a wajen ‘yan Najeriya.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel