An zuba ‘yan sanda 600 a kan titin Abuja zuwa Kaduna

An zuba ‘yan sanda 600 a kan titin Abuja zuwa Kaduna

- Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta zuba dakarun ‘yan sanda 600 a fadin titin Abuja zuwa Kaduna

- An zuba su ne domin magance yawan garkuwa da mutane da ake fama da shi a kasar musamman a wannan hanya

- Sufeto Janar na 'yan sanda ya ce hakkin jami'an tsaro ne ba al'umma kariya

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta zuba dakarun ‘yan sanda 600 a fadin titin Abuja zuwa Kaduna. Mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sanda, DIG Habila Joshak ne ya bayyana haka, a lokacin da ya ke kaddamar da rundunar ‘yan sandan na musamman, a kauyen Rijana, kan titin Kaduna zuwa Abuja, a jihar Kaduna.

Joshak ya sanar da cewa ‘yan sanda 500 aka baza, saura 100 kuma jami’an ‘yan sandan kwantar da tarzoma ne daga sashen leken asiri na fannin tsaron rundunar ‘yan sanda.

Sufeto Janar na ‘yan sanda Ibrahim Idris ne ya bayar da umarnin baza jami’an tsaron domin kara tabbatar da kare rayukan matafiya a kan titin Abuja zuwa Kaduna.

KU KARANTA KUMA: Abin kunya: Saudi ta aikowa Najeriya dabino sadaka amma an saida

An zuba ‘yan sanda 600 a kan titin Abuja zuwa Kaduna

An zuba ‘yan sanda 600 a kan titin Abuja zuwa Kaduna

Ya ce hakki ne da ya rataya a kan wuyan jami’an tsaro na kare rayuka, dukiyoyi da lafiyar jama’a, shi ya sa aka zabo wadannan zaratan ‘yan sanda daga cikin zaratan da ke yaki da kakkabe Boko Haram da sauran su.

Daga nan sai Mataimakin Sufeton ya yi horo ga jami’an tsaron da su yi aikin su da gaskiya da kuma kishi, wajen kare rayukan jam’a da kuma tabbatar da tsaro a kan titin Abuja zuwa Kaduna da sauran wuraren da ke kewaye da hanyar.

Ya kuma ce za su yi aiki kafada-da-kafada da sauran jami’an tsaron da ba ‘yan sanda ba, wajen ganin an kakkabe matsalar sata da garkuwa da matafiya da ya zama ruwan-dare a kan titin.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel