Musulman da suka tashi cin Sahur suka ceci rayukan Jama’a a gobaran cikin dare

Musulman da suka tashi cin Sahur suka ceci rayukan Jama’a a gobaran cikin dare

Mutane mabiya addinin Islaman da suka tashi domin sannanta sunnan Sahur sun ceci rayukan mutane yayinda wata gobara ta balle a gida mai tsauni 27 mai suna Grenfell Tower.

Akalla mutane 7 suka rasa rayukansu kuma mutane 50 sun jikkata kuma suna asibotoci daban-daban. Gobarar ta fara ne misalin karfe 1.15 na dare yayinda kowa yayi bacci face Musulmai masu raya daren Ramadana.

Wata mata ta bayyanawa HuffPost UK cewa: “Yaran Musulmai suka ceci rayukan mutane. Sun zagaya suna kwankwasa kofofin mutane. Mun godewa Allah ga Ramadana”

Khalid Suleman Ahmed, wani mazaunin gidan yace baccin tashin da yayi domin cin sahur da shima yana ciki yaa diban minshar.

Gobarar Landan: Mutan Landan sun ci alfarman azumin Ramadana yayinda Musulman da suka tashi cin Sahur suka ceci rayukan Jama’a

Gobarar Landan: Mutan Landan sun ci alfarman azumin Ramadana yayinda Musulman da suka tashi cin Sahur suka ceci rayukan Jama’a

Yayinda ya ga hayaki ya fara tasowa, da wuri ya fara buga kofofin makwabta domin tayar da su.

Yace: “Babu wani gargadi da na gani. Ina buga PlayStation sauraron lokacin Sahur sai na fara shinshinan hayaki. Sai na tashi na duba taga dakina nag a tsauni na 7 na hayaki.

KU KARANTA: An hana Melaye yin wani taro a jihar Kogi

“Sai na tashi yar uwata muka fara kwankwasa kofan makwabta. Dukkansu sun tashi face 2.”

https://web.facebook.com/naijcomhausa/?ref=bookmarks

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Obasanjo

Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Obasanjo

Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Obasanjo
NAIJ.com
Mailfire view pixel