Hajjin bana: Maniyyata 200 ne kawai suka kammala biyar kudin kujerunsu a jihar Filato

Hajjin bana: Maniyyata 200 ne kawai suka kammala biyar kudin kujerunsu a jihar Filato

- Hukumar dake kula da jin dadin Alhazai na jihar Filato ta bayyana yawan maniyyata da suka kammala biyan kudin su

- Ya ce zuwa yanzu mutane 200 ne suka kammala cikin 600

- Daga karshe sun bayyana cewa jihar bata tsayar da ranar rufe karban kudaden ba

Hukumar kula da jin dadin Alhazai na jihar Filato ta bayyana cewa a cikin maniyyata 600 da suka fara tariyan biyan kudin aikin hajji na bana daga jihar mutane 200 ne kawai suka iya kamala biyan kudadensu zuwa yanzu.

KU KARANTA KUMA: Abin kunya: Saudi ta aikowa Najeriya dabino sadaka amma an saida

Wani jami’i a hukumar Wada Haruna, ya sanar da cewa har yanzu gwamnatin jihar bata tsayar da ranar rufe karban kudaden maniyyan da basu karisa cika kudaden nasu ba.

Haruna ya kara da cewa gwamnati ta ba jihar kujeru 1200 ne a hajin bana sannan Fulani makiyaya ne suka fi yawa cikin maniyyatar jihar.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel