Abin kunya: Saudi ta aikowa Najeriya dabino sadaka amma an saida

Abin kunya: Saudi ta aikowa Najeriya dabino sadaka amma an saida

– Kasar Saudi ta aikowa Najeriya sadakar dabino na azumi

– Sai ga shi yanzu ana saida wannan dabino a kasuwa

– Ministar kasar da tayi alkawarin za a rabawa ‘yan gudun hijira

Wannan abin kunya sai ace da me yayi kama

Najeriya dai ta kara buga abin kunya a idon Duniya

An aikowa Najeriya sadaka amma an kai kasuwa domin a ci riba

Abin kunya: Saudi ta aikowa Najeriya dabino sadaka amma an saida

Saudi ta aikowa Najeriya ton 200 na dabino an saida

Kwanakin baya kun ji cewa Ofishin Jakadancin Saudiya a Najeriya ya bayyana cewa kasar ta aikowa Najeriya tulin dabino domin buda baki. Sai dai yanzu haka wannan dabino na yawo a kasuwa cikin Abuja ana saidawa.

KU KARANTA: Wani yace ko a keke ne sai an kara zaben Buhari

Hajiya Khadija Bukar Abba Ibrahim

Karamar Ministar harkokin kasar wajen Najeriya

Ministar harkokin kasar waje Hajiya Khadija Bukar Abba Ibrahim tayi alkawari da fari cewa za a raba kayan ne musamman ga ‘Yan gudun Hijira da ke Yankin Arewa maso gabas sai dai ba haka abin ya kasance ba.

Gwamnatin Tarayya ta bakin Ma’aikatar harkokin kasar wajen ta ba Kasar Saudiya hakuri inda tace wasu bata-gari ne su ka yi gaba da dabinon bayan an kai inda ya kamata a raba su domin su samu abin Duniya.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Jam'iyya za su kawo karshen matsalolin siyasar Najeriya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel