Bayan Kotu ta wanke Saraki ka ji yadda aka kare da Orubebe

Bayan Kotu ta wanke Saraki ka ji yadda aka kare da Orubebe

– Kotun daukaka kara ta wanke tsohon Ministan Neja-Delta

– Kotun CCT ta samu Mista GodsdayOrubebe da laifi

– Sai dai babban Kotu tace Orubebe bai aikata wani ba daidai ba

Kotu ta wanke Bukola Saraki da Godsday Orubebe a rana guda. Da fari an samu tsohon Minista Orubebe da laifi. Yanzu kotun daukaka kara tace Orubebe mai gaskiya ne

Bayan Kotu ta wanke Saraki ka ji yadda aka kare da Orubebe

Ka ji yadda shari’ar Orubebe da Gwamnati ta kare

Tsohon Ministan Neja-Delta lokacin Shugaba Goodluck Jonathan watau Godsday Elder Orubebe ya sha a Kotu inda aka wanke sa tas daga zargi. Hakan dai na zuwa ne bayan Kotu ta wanke Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki.

KU KARANTA: Inyamurai sun ce ba su shirya yaki ba

Bayan Kotu ta wanke Saraki ka ji yadda aka kare da Orubebe

Shari’ar Orubebe da Gwamnati a Kotun CCT

Da fari dai Alkali Danladi Umar na Kotun CCT ya bayyana cewa Orubebe ya ki bayyana wasu kadarorin da ya mallaka don haka ya aikata laifi. Sai dai yanzu Kotun daukaka kara da Abuja yace sam Mista Orubebe bai yi wani laifi ba.

Alkali Abdu Aboki ya bayyana cewa tsohon Ministan ya riga ya saida kadarorin da ake magana tuni don haka babu dalilin kama sa. Wasu dai na ganin cewa shirin yaki da cin hanci da Gwamnatin Buhari take yi na gamuwa da matsala tun da aka wanke Bukola Saraki.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

An yaye Sojojin saman Najeriya [Bidiyo]

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel