Kura-kurai 10 da Gwamnatin Buhari ta yi wanda ya kai arzikin Najeriya durkushewa

Kura-kurai 10 da Gwamnatin Buhari ta yi wanda ya kai arzikin Najeriya durkushewa

- An sami shekaru biyu kenan a mulkin jam'iyyar APC

- Anyi rawar gani a mulkin Buhari

- An tafka kura kurai a mulkin Buhari

A lokacin da ake waiwaye domin duba yadda ta kasance, kuma ake bin kadin alkawurra da 'yan siyasa suka daukar wa al'umma, an sami da yawa daga talakawa, suna yabawa da abin da suka ce aikin gwamnati na alheri, inda wasu kuma, suke tir, da gajiyawa da salo na mulkin shugaba Buhari.

Mafi akasarin 'yan Najeriya na ganin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari bata tsinana masu komai ba ta fannin jin dadin rayuwa a kasar.

KU KARANTA KUMA: Abin kunya: Saudi ta aikowa Najeriya dabino sadaka amma an saida

Kura-kurai 10 da Gwamnatin Buhari tayi wanda ya kai arzikin Najeriya durkushewa

Kura-kurai 10 da Gwamnatin Buhari tayi wanda ya kai arzikin Najeriya durkushewa

NAIJ.com ta zakulo muku kura-kurai guda 10 da wasu yan Najeriya ke ganin an tafka a wannan tafiya ta shugabancin Buhari.

Ku duba a kasa a jere:

1. Rashin dora ministoci a kan kari, wanda ya hana jama'a da kasuwanni sanin alkiblar gwamnati shekara kusan daya bayan zabe. Wadanda suka ci zabe tun watan Maris, suka kai watan Nuwamba basu hada gwamnati ba, lallai basu shirya ba.

2. Kokarin sai fadar gwamnati ta kakaba wa majalisun tarayya shuwagabannin ta. Wannan ya zubar wa gwamnatin shugaba Buhari aji, inda ko jam'iyya da ta sha kaye ta PDP sai da ta dara, saboda kasa wa da fadar shugaban kasa tayi, ta dora wadanda take so.

3. Yaki da cin hanci ya zamo kamar bi-ta-da kullin siyasa, inda wasu ake ganin sun zama shafaffu da mai ba'a ta tasu, amma 'yan adawa sun sha dandana kudarsu.

4. Tattare dukkan kudaden gwamnati da ke hannun hukumomi da bankuna, a kulle su a babban bankin kasa, wannan ya zafafa radadin talauci a tsakanin jama'a. Kudaden da aka riga aka yi kasafin kudi dasu a lokacin tsohuwar Gwamnati bai kamata sabuwar gwamnati ta hana kashe su ba.

5. Karfa-karfa kan yadda Naira da Dala zata kasance a kasuwannin duniya. Idan aka ce gwamati ce zata saka farashin kudin kasa, ba wai yadda kasuwa ta kaya ba, wannan zai kawo tsaiko da yawan banbancin farashi a tsakanin kasuwanni.

6. Kin bin umarnin kotuna. A lokuta da dama ana dauka cewa kowanne bangare na gwamnati a dimokuradiyya yana da iya nasa ikon, amma sai gashi umarnin kotu ya ki aiwatuwa a kan wasu kamammu.

7. hana babban banki samar da dala ga matafiya da 'yan kasuwa. Wannan yasa jama'a neman dala ta kowacce hanya, wanda a cikin shekara daya dalar ta kai N500 tun daga N200. Sai kuma gashi mukaddashin shugaban kasa ya saka ana sayar da dalar mako-mako, wanda ya daidaita tsaiko da rashin kudaden wajen.

8. Batun kin sauya ministoci ma ya kawo irin wannan tsaiko, inda har yanzu wadanda aka nada sune suke kan kujerunsu, babu chanji babu musaya.

9. Kasa gama nade-naden mukamai duk da an kai shekaru biyu ana mulki. A kasashe da yawa babu jakadu, haka nan wasu mukamai na hukumomin gwamnati har yanzu babu wanda aka nada ya shugabance su shekara biyu. Wasu nade-naden kuma anyi su a makare sosai.

10. Rashin ziyarar jihohin da yaki da Boko Haram ta daidaita, duk da a baya suma sun kushe shugaba Goodluck Jonathan kan kasa zuwa Maiduguri, har yanzu bayan shekaru biyu, ba'a ga shugaba Buhari a wadannan jihohin da yaki ya tagayyara ba.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel