Shin ko Shugaba Buhari zai iya karasa wa'adin mulkinsa?

Shin ko Shugaba Buhari zai iya karasa wa'adin mulkinsa?

- An shafe kusan duk shekarar nan shugaba Buhari baya iya aiki

- Shugaba Buhari yana birnin landan tsawon watanni yana jinya

- Ya mika mulki ga mataimakinsa Farfesa Osinbajo

Ya zuwa yanzu dai babu wanda ya saka shugaba Buhari a ido, yawan makonni 5 da shugaban ya kai a birnin Landan, wasu masu ganin kwakwap ma na ganin cewa ko iyalinsa da ta ziyarce shi a asibiti bata sami ganinsa ba.

A shekaru irin na tsufa, baka rasa dan dagaji da rashin kwari da rashin lafiya a tattare da jikin dan-adam, wannan ne ma ya saka makusantan shugaba Buhari ke cewa cutar tsufa ce ke damun shugaban ba wai wata babbar rashin lafiya ba.

KU KARANTA KUMA: Abin kunya: Saudi ta aikowa Najeriya dabino sadaka amma an saida

Mutanen Najeriya dai sun zabi Buhari mai shekaru 74 a duniya, saboda nagartar da suka gano a tattare da shi, karfin halinsa, jarumtar sa, gaskiyarsa, da ma yanayin da kasa ta shiga na yaki. An dai gagara shawo kan matsaloli daban daban, a waccan gwamnati, inda jama'a suka gaji da salon irin wancan mulki, suka kawar da gwamnatin.

Shin ko Shugaba Buhari zai iya karasa wa'adin mulkinsa?

Shin ko Shugaba Buhari zai iya karasa wa'adin mulkinsa?

Sai dai kash! Domin irin lokacin samartaka da karfin iko na tsohon shugaban ya wuce, a baya yayi rawar gani a matsayin shugaba, a matsayin gwamna, da ma minista, sa'annan kuma a matsayin shugaban hukumar PTF, mai tara rarar man fetur ta iyar da aiki da ake matukar bukata a kasa. Yayi, an gani, kuma har yanzu ana morar abubuwan da wannan shiri ya kawo.

A lokutan zabe na 2003, 2007, da ma 2011, shugaban ya nemi takara, amma ya sha kaye a hannun jam'iyya mai mulki a lokacin wato PDP, wannan tsakani, shekaru kusan 13 kenan kafin ya samu ya ci zabe, wanda hakan ke nufin karfinsa ya kara kasa fiye da lokacin samartaka. Don haka, bayan hawansa mulki, yace abubuwa sun masa yawa, karfin ba kamar na da bane, don haka ayi hakuri zai ja a hankali ba sauri.

Gaba daya dai a yanzu ana jin cewa shugaban ba lallai ya iya karasa ko kuma neman takara a karo na biyu ba a wa'adin mulkinsa, saboda ya samu ya dubi lafiyarsa da kyau. A watanni 6 dai na wannan shekara, shugaban bayyi wani aiki ba, inda kusan duka lokacin, mukaddashinsa ne ke tafiyar da gwamnati.

Wannan yasa mutane ke ganin kamar dai ba zai iya samun kwarin karasa aikin ba, sai dai ya bari a karasa masa, ko kuma ya ma yi murabus don ya huta, ya baiwa wadanda zasu iya su ci gaba.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel