'N750,000 da na saka a asusun alkali ba cin hanci bane, gudummawar asibiti ce'

'N750,000 da na saka a asusun alkali ba cin hanci bane, gudummawar asibiti ce'

- Ana yawan zargin alkalai da karbar cin hanci a Najeriya

- Ba'a taba jefa ko daya daga wadanda ake zargi fursuna ba, duk da girman shaidar da ake kama su da ita

- An tuhumi lauya da saka kusan muliyan daya a asusun alkali

A irin kesa-kesai da ake samu a kotunan kasar nan na cin hanci da rashawa, an kama wasu makudan kudi da suka kai N750,000 a asusun wani babban alkali mai suna Justice Nasiru Yinusa, wanda wani babban lauya mai suna Joseph Nwobike, ya saka masa.

Sai dai da aka kai karar batun babbar kotu da ke Ikeja a jihar Legas, sai kawai lauyan ya kada baki yace ai shi ba fa cin hanci ya bayar ba, a'a, kudin maganin mahaifiyar alkali da bata jin dadi ya biya, saboda yana tausayawa alkalin.

A zahiri dai, alkalin ya kamata ace ya fi lauyan albashi, da kudi, ya kamata kuma a gane me yasa ya biya kudi a asusun shi Jojin, duk da cewa akwai kararraki da ake aiki a kansu a kotun, wannan ya nuna akwai kanshin gaskiya cewa rashawa ce kawai lauyan ya bayar don ya sami hukunci mai kyau daga alkali Yinusa, wanda shi kuma yayi gum da bakinsa bayan da yaji shigar kudi asusu.

'N750,000 da na saka a asusun alkali ba cin hanci bane, gudummawar asibiti ce'

'N750,000 da na saka a asusun alkali ba cin hanci bane, gudummawar asibiti ce'

Shaidar EFCC, Malam Daniel Danladi, ya ce shi kuma a nasa sanin kudin harda gudummawar ginin laburare da lauyan ya biya, amma wai ba da niyar cin hanci bane.

"Kawai na sami kira ne daga wani ma'aikacin EFCC da yace suna bukatar ganina, wanda yace sunan sa Mal. Zakari, sai dai kawai ina isa wurinsu sai na sami takarda da ke nuna kudi N750,000 da na sakawa alkalin a bankin sa na UBA," lauyan ya fadi.

Za dai mu iya cewa anki cin biri an ci dila, ko ya zata kaya a irin wannan shari'a? Ganin cewa komai girman hujja daga karshe babu wanda ke shiga hannu? Sai ku biyo mu, domin zamu bi muku labarin har karshe...

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Kalli wannan bidiyo da NAIJ.com ta kawo maku na tambaya kan yadda zakayi idan ka ji shigar kudi naira miliyan dari asusun ka na banki

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi

Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi

Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi
NAIJ.com
Mailfire view pixel