Cewa sukayi zasu babbake ni da rai na - Limamin coci da aka sace

Cewa sukayi zasu babbake ni da rai na - Limamin coci da aka sace

- Sace-sace don fansar kudi da mutane ta zama ruwan dare a najeriya

- An cafke limamin coci a hanyarsa ta zuwa taro

- Yace addu'o'in da ya dinga yi ne suka cece shi

Shugaban cocin Jesuits ta jihar Edo, Pastor Samuel Okwoidegbe, ya ce da kyar da jibi yasha daga hannun yan fashi masu garkuwa da mutane, a hanyarsa ta zuwa taron mujami'arsu a garin Anisha ta jihar Anambara. Ya bayyana wadanda suka sace shi da cewa fulani ne masu manyan makamai.

Cif Samuel, ya ce: "muna cikin tafiya sai muka ji harbi, muna waigawa sai muka ga motoci na ribas, kafin muma mu yi tuni wani da daurarriyar fuska da bindiga ya fito a gabanmu, ya kuma ce mu fito, haka ma motar bayanmu marsandi, itama aka fitar da mutum biyu.

"Sun luluka damu cikin daji, inda daya daga waccan motar ya kasa sassarfar da suke yi, suka sake shi suka ce ya tafi. Amma sai fa da suka yanka masa kafa wai kar ya isa gari da wuri ya tona su. Sun tambaye mu waya don kira su karbi fansa, basu samu tawa ba, suka rufe ni da duka, suka ce kone ni da raina zasuyi, ba taba ganin bala'i irin wannan ba.

KU KARANTA KUMA: Abin kunya: Saudi ta aikowa Najeriya dabino sadaka amma an saida

Ya kara da cewa: "A karshe dai anyi anfani da wayar wanda aka kama mu tare, aka kira cocin mu, daga nan sai kawai suka sake mu suka kama gabansu, na san dai addu'a ce ta cece mu, nasan kuma ubangiji na yana tare da ni."

A yanzu dai barayi sun gane kasuwar sata da garkuwa da manyan mutane, inda suke karbar makudan kudade daga hannun makusantansu kafin su sake su, hukumomi na iya kokarinsu, amma sun kasa hana lamarin.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel