Masu sahur ne suka ceci mutane a gobarar London

Masu sahur ne suka ceci mutane a gobarar London

- Ya zuwa yanzu dai, mutum 12 ne suka rasa rayukansu 70 kuma suka jikkata

- Anyi sa'ar ceto mutane da yawa dalilin wasu sun farka sahur a lokacin

A birnin Landan an sami wata mummunar gobara da ta cinye wani dogon gini makare da mutane, amma abin yazo da sauki domin lokacin wasu sun farka sahur, inda suka yi kokarin tashin jama'a don su tsira da rayukansu.

A hira da masu gani da ido, an sami labarin cewa sai da aka kwanta bacci sannan wutar ta tashi, kuma cikin kankanin lokaci ta cinye komai kurmus, a dogon ginin mai hawa 24.

An dai sami wasu suna wullo 'ya'yansu, wasu kuma suna kulla zannuwa don dira waje daga ginin, wasu kuma har yanzu ba'a san inda suke ba.

Masu sahur ne suka ceci mutane a gobarar London

Masu sahur ne suka ceci mutane a gobarar London

Matashi Khalid Suleiman dan shekara 20, yace yana cikin wasan sa game din play station, yana jiran lokacin sahur, kawai sai yaji kauri, nan da nan kuma ya farga ya tashi ya duba.

"Babu wani kararrawa ko jiniya ta gobara, jama'a na ta bacci, sai kawai na ji kauri, na tashi nabi duk gidajen ginin ina bugawa ina tashin jama'a don su tsira, ba don haka ba da abin ya kazanta", cewar sa.

Har ya zuwa yanzu dai 'yan kwana-kwana na kokarin kashe wutar, kuma ana neman jama'a da yawa, cikin zullumi.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel