Zirga-zirga ta tsaya cik tsakanin kudu da arewa maso gabashin kasar

Zirga-zirga ta tsaya cik tsakanin kudu da arewa maso gabashin kasar

- Zirga zirga ta tsaya cik tsakanin kudancin Najeriya da arewa maso yammacin kasar sabili da rushewar wasu gada a jihar Neja

- A na musayar fasinjoji da kananan motocin da fasinja da suka fito daga Legas da wanda suka fito daga arewa maso yammacin kasar

- Kwamishinan yada Labarai ta jihar Neja ya ce cikin wata daya idan gwamnatin tarayya ta ga dama zata iya gyara gadoji biyu da suka rushe

Zirga zirga ta tsaya cik tsakanin kudancin Najeriya da arewa maso yammacin kasar, bayan da wasu muhimman gadoji biyu suka rufta a jihar Neja.

Ta baya bayan nan itace gadar da take Tatabu-inda masu kananan motocin dibar fasinja da suka fito daga Legas, suke musayar fasinjoji da motoci da suka fito daga arewa maso yammacin kasar.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, daya gadar data rufta itace wacce take Bakane. Al’amarin ya shafi harda zirga-zirgan jirgin kasa daga Legas zuwa Kano.

Zirga-zirga ta tsaya cik tsakanin kudu da arewa maso gabashin kasar

Zirga-zirga motoci ta tsaya cik tsakanin kudu da arewa maso gabashin Najeriya

Masu manyan motocin dakon kaya sune wannan matsala tafi shafa domin ba zasu iya zuwa inda suka dosa ba saboda wannan lamari.

KU KARANTA: Ana zargin Saraki da baiwa alkalin kotun CCT cin hancin $2m domin wanke shi

Hukumomi a jihar ta Neja ta bakin kwamishinan yada Labarai, Jonathan Vatsa, ya ce basu da karfin yin komi kan ayyukan gyara hanyoyin domin basu da kudi, kuma hakkin gwamnatin tarayya ne. Vatsa ya yi amfani da wannan damar wajen yin kira ga gwamnatin tarayya da ta dauki matakin gaggawa na magance wannan lamari.

Ya ce a cikin wata daya idan gwamnatin ta ga dama zata magance wannan matsala.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Jerin nasarori shugaba Buhari a cikin shekaru biyu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC
NAIJ.com
Mailfire view pixel