Sojojin Najeriya ne suka kone mana kauye ba Boko Haram ba - Mazauna jihar Borno

Sojojin Najeriya ne suka kone mana kauye ba Boko Haram ba - Mazauna jihar Borno

- Ana zargin soji da kone kauye kurmus bayan Boko Haram sun kai hari Maiduguri

- Sojojin sunce mutan garin suna taimakawa Boko Haram

- Sarakuna sun ce sun kai rahoton isowar mayakabBoko haram aka ki kulawa

A ci gaba da ake da yaki da Boko Haram, a gabas ta arewar Najeriya, mazauna wani kauye a wajen garin Maiduguri sun zargi sojojin Najeriya da kone musu kauye bayan sun basu wa'adin su tashi su bar wurin, inda suka ce suna zargin su da baiwa mayakan Boko Haram mafaka da mashiga izuwa garin Maiduguri don kai hari.

Garin Ali-Dawari ne dai mayakan Boko Haram din suka yi amfani dashi, suka shiga birnin Maiduguri a makon jiya, inda suka kai hari kuma suka fice.

Amma kwanaki uku da harin sau sojoji suka yi wa garin kawanya, a cewar mazauna garin suka basu sa'o'i biyu su bar garin, inda suka cinna wa garin wuta, bisa wai zargin cewa mutan garin sun bari Boko Haram tayi amfani da garin don kai hari.

KU KARANTA KUMA: Ana neman ‘Dan Marigayi Shugaba Gaddafi na Kasar Libiya ruwa a jallo

'Sojojin Najeriya ne suka kone mana kauye ba Boko Haram ba'

'Sojojin Najeriya ne suka kone mana kauye ba Boko Haram ba'

A cewar mutanen garin kuma, Bulama Mustapha, da Bulama Umar, sunce sun kai rahoto ga sojojin da ke girke a wajen garin nasu yayin da suka gano mayakan Boko Haram, amma wai sai sojojin suka cika wandon su da iska suka tsere, wayar kuma da aka basu, wadda suke kira, aka kashe ta.

"Akwai Kaftin Sa'idu, wanda shine shugaban bataliyar sojin da aka ajje mana a yankin, mutanenmu na civilian jtf sun masa waya amma bai dauka ba, sai dai yazo ya kore mu ya kone mana gari."

Wata dattijuwa dai, ta ce babu abinda suka bar mata, har dan abincinta na azumi da ta ajje sojojin sun kone mata shi. Wani mazaunin garin kuma yace kafin sojojin su saka wuta sai da suka cika babbar motarsu da dukiya da kayan mutanen garin.

Kira don tabbatar da wadannan zargi dai bai sami amsawa ba daga hukumar soji mai aiki a yankin ya zuwa yanzu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi

Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi

Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi
NAIJ.com
Mailfire view pixel