Arewa zata sake zaben Buhari a 2019 - Dattijon Arewa, Mohammed Alhaji Yakubu

Arewa zata sake zaben Buhari a 2019 - Dattijon Arewa, Mohammed Alhaji Yakubu

Wani mamban kungiyar mashawartan Arewa wato Arewa Consultative Forum, ACF, Mohammed Alhaji Yakubu, yace arewacin Najeriya zata zabi shugaba Muhammadu Buhari a 2019 ko yana kan keke mai wili.

Yakubu ya bayyana wannan ne yayinda yake sukan wasu yankuna masu cewa shugaban kasan yayi murabus saboda rashin lafiyarsa.

Yayinda yake magana da jaridar Sun, Yakubu yace, “Ban zan bashi shawaran yayi murabus ba. Zaku tuna cewa lokacin da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bukaci Umaru Musa Yaradua da yayi murabus, na gabatar da hira da jaridarku cewa a matsayina na shugaban kungiyar matasan arewa, ko Yar’adua na kan keken hannu ne zamu goyi bayansa. Amma sai yayi wafati."

Arewa zata zabi Buhari ko a keke mai wili 2019 – Dattijon Arewa, Mohammed Alhaji Yakubu

Arewa zata zabi Buhari ko a keke mai wili 2019 – Dattijon Arewa, Mohammed Alhaji Yakubu

“Hakazalika ina sake maimaitawa a yau cewa kada Buhari yayi murabus, ko yana ka keken hannun ne, arewa da mutanen Najeriya zasu zabe shi a 2019.

“Bani tunanin ya dace mutane su dinga cin mutunci Buhari da cewa yayi murabus. Bai dace ba sam.”

KU KARANTA: Yadda Buhari ya karrama inyamuri yayinda yake sabis

“Akwai jadawalin zabe, idan b aka son shi, ka zabi wani lokacin zabe, amma ba zan goyi bayan duk wanda zai ci mutuncin Buhari ba. Muddin yana nan da rai, bai dace a bukaceshi da murabus ba.”

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel