Faransa da Birtaniya za su dakile ta'addanci a Intanet

Faransa da Birtaniya za su dakile ta'addanci a Intanet

- Kasar Faransa da Birtaniya sun alwashin dakile ta’addaci a kafofin sadarwa na zamani

- Birtaniya tace ta fara tattaunawa da kamfanonin kafofin sadarwar na zamani domin dakile yada farfagandar ‘yan ta’adda da ke tasiri a zukatan matasa

- kasashen biyu sun ce za a dauka matakan da suka dace domin dakile ayyukan ta’addanci

Kasashen Faransa da Birtaniya sun bayyana shirinsu na yin aiki tare domin murkushe masu amfani da kafofin sadarwa na zamani wajen cusa tsattsauriyar akida ga matasa.

Bayan ganawar da shugabanin kasashen biyu Emmanuel Macron da Theresa May suka yi a birnin Paris, Macron ya ce, kasashen biyu sun yanke hukuncin cewar masu kula da kafofin sada zumunta ba sa daukan matakan da suka dace domin dakile ayyukan ta’addanci.

KU KARANTA: Mutane 6 sun mutu, 20 sun jikkata a yayin gobarar bene mai hawa 27 (Hotuna)

A nata bangare, Theresa May, ta ce gwamnatinta ta fara tattaunawa da kamfanonin kafofin sadarwar na zamani domin dakile yada farfagandar ‘yan ta’adda da ke tasiri a zukatan matasa.

Faransa da Birtaniya za su dakile ta'addanci a Intanet

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron da na Birtaniya Theresa May

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, wannan na zuwa ne bayan hare-haren ta’addancin da aka kai wa Birtaniya a biranen London da Manchester, abin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama da suka hada da kananan yara.

Ita ma dai Faransa na fama da barazanar ‘yan ta’adda da suka kai ma ta wani kazamin hari a shekarar 2015, in da fiye da mutane 250 suka mutu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yaya za ka ji idan shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bamme Boko Haram kamar Siriya?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC
NAIJ.com
Mailfire view pixel