Goron Ramadan: Falalar I’itikafi a cikin watan Ramadan

Goron Ramadan: Falalar I’itikafi a cikin watan Ramadan

– Musulmai na azumi a fadin Duniya a cikin wannan wata

– Akwai matukar lada ga wanda ya kebe a masallaci

– Wannan kebewar ake kira I’itikafi a Addini

Akwai matukar lada ga wanda ya samu yin I’itikafi a cikin wannan wata. Manzon Allah SWT ya kan zauna a cikin masallaci yayi ta ibada. Ana so Musulmai su yi koyi da wannan ibada na Manzon Allah.

Goron Ramadan: Falalar I’itikafi a cikin watan Ramadan

Shugabannin Najeriya na addu'a a masallaci

Yayin da ake azumin watan Ramadan yana daga cikin ayyukan lada shiga I’itikafi watau kebawa a Masallaci ba a wani aiki face salloli da karatun Al-kur’ani mai girma. A cikin Bukhari ya tabbata cewa Manzo SAW na yin I’itikafi a irin wannan lokaci na karshen Ramadan.

KU KARANTA: Gwamnan Bauchi ya wuce Saudiya domin ganin likita

Goron Ramadan: Falalar I’itikafi a cikin watan Ramadan

Ana son I’itikafi a goman karshen Ramadan

Akwai Hadisi daga Abdullahi ‘Dan gidan Abbas RA daga Manzo SAW da ke cewa duk wanda yayi I’itikafi a kwanaki goma na karshen Ramadan ba zai shiga wutar Jahannama ba. Wannan Hadisi dai Imam Tabarani ya kawo shi.

Kwanaki kun ji cewa Mista Olu Aijotan wani masanin harkar lafiya ya bayyana abin da ya dace mai azumi ya rika ci a wannan wata daga ciki dai akwai ganye da abinci mai gina jiki.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kaya sun yi tsada lokacin Azumin Ramadan

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel