Musa: A yanzu ina cikin farin ciki bayan aurena na biyu

Musa: A yanzu ina cikin farin ciki bayan aurena na biyu

- Ahmed Musa ya ce sakin tsohuwar matarsa Jamila shine daidai

- Jarumin kwallon kafa kuma dan kungiyar Super Eagles na da ‘ya’ya biyu tare da tsohuwar matarsa

- Musa ya auri sabuwar mata Juliet Adeh a watan da ya gabata

Jarumin kwallon kafa na kungiyar Super Eagles Ahmed Musa ya ce sakin tsohuwar matar sa da auren sabuwa ya kawo masa farin ciki.

Jarumin ya fada ma Complete Sports cewa ya wahala saboda auren sa da Jamila.

KU KARANTA KUMA: Matar da ta fi kowa tsufa a duniya ta mutu tana da shekaru 134 (HOTUNA)

Musa: A yanzu ina cikin farin ciki bayan aurena na biyu

Ahmed Musa da amaryar sa

Musa mai shekaru 24, ya saki matarsa da suka shafe tsawon shekaru hudu tare kuma uwar ‘ya’yansa guda biyu, Jamila, kafin ya auri Juliet Adeh a watan da ya gabata.

Musa: A yanzu ina cikin farin ciki bayan aurena na biyu

Musa da tsohuwar matarsa Jamila

“Aure ba sabon abu bane a gare ni amma na yi imani cewa yunkuri ne mai kyau a lokacin da na yi,” Musa ya fada ma Complete Sport.

“Abun da ya wuce a baya ya wuce. Ina farin ciki a yanzu sannan kuma ina tunani da kyau kuma zan mayar da hankali a wasa na wanda ya dan samu tangarda."

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel