Mutane 6 sun mutu, 20 sun jikkata a yayin gobarar bene mai hawa 27 (Hotuna)

Mutane 6 sun mutu, 20 sun jikkata a yayin gobarar bene mai hawa 27 (Hotuna)

- An tafka asarar rayuka da dukiyoyi a yayin gobarar bene mai hawa 27 a Landan

- Gidan ya kwashe awanni da dama yana ci ba kakkauyawa

An tafka asarar rayukan Jama’a da dama a lokacin da gobara ta tashi a wani katafaren gidan sama a birnin Landan mai hawa 27, mai suna Greenfell Tower.

Rahotannin da suka ishe NAIJ.com sun bayyana cewa sama da jami’an kwana kwana 200 ne suka isa gidan suna kashe wutar, tare da hawa dogayen tsani domin ceto mutanen gidan.

KU KARANTA: Zaman tattaunawa tsakanin shugabannin Arewa da Osinbajo (HOTUNA)

A jawabin kwamishinan kwana-kwana na garin Landan, Dany Cotton yace jama’a da dama sun rigamu gidan gaskiya, sai dai bai iya tantance yawansu ba, haka zalika Dany yace bai taba ganin irin wannan jafa’i ba tun da ya fara aikin bada agajin gaggawa.

Mutane 6 sun mutu, 20 sun jikkata a yayin gobarar bene mai hawa 27 (Hotuna)

Gobarar bene mai hawa 27

Amma jaridar The Guardian ta kasar Ingila ta bayar da wani rahoto dake nuna yawan wadanda suka rasu ya kai 6, 20 kuma an garzaya dasu asibiti domin samun kulawa.

Mutane 6 sun mutu, 20 sun jikkata a yayin gobarar bene mai hawa 27 (Hotuna)

Gobarar bene mai hawa 27

Sai dai majiyoyi da daman a ganin da yiwuwar wannan katafaren gini ya rushe saboda tsananin wuta daya ci, da kuma awannin da wutar ta kwashe tana ci. Sai dai kuma, ba’a tabbatar da dalilin tashin wutar ba.

Mutane 6 sun mutu, 20 sun jikkata a yayin gobarar bene mai hawa 27 (Hotuna)

Yadda gidan yaci

Mutane 6 sun mutu, 20 sun jikkata a yayin gobarar bene mai hawa 27 (Hotuna)

Wayewar gari

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Miliyan a asusun ka, me zaka yi?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel