Kuyi hakuri yan uwa inyamurai, bamu shirya wa wani yakin ba - Gwamna Okorocha

Kuyi hakuri yan uwa inyamurai, bamu shirya wa wani yakin ba - Gwamna Okorocha

- Gwamnan jahar Imo Rochas Okorocha ya gargadi kungiyar da ke fafutikar samar da Biafra (IPOB) da ta guji neman barkewa daga Nijeriya, inda ya ce ‘yan kabilar Inyamurai ba su shirya wa wani yakin ba.

- Gwamnan ya mika gargadin ne a wani taron manema labarai a fadar gwamnatin sa da ke Owerri a jiya Talata.

Haka kuma ya yi kira ga kungiyar MASSOB da sauran Inyamuran Nijeriya da ke kasashen waje wadanda ke nuna goyon baya ga fafutikar da su dakata a haka.

Ya shawarci matasan Igbo da su mayar da hankalin su ga bangaren inganta tattalin arzikin mutanen su, ba wajen neman sabuwar kasa ba.

Kuyi hakuri yan uwa inyamurai, bamu shirya wa wani yakin ba - Gwamna Okorocha

Kuyi hakuri yan uwa inyamurai, bamu shirya wa wani yakin ba - Gwamna Okorocha

NAIJ.com ta samu labarin cewa kuma game da matakin zama a gida da kungiyoyin suka umarta a ranar 30 ga watan da ya gabata, Okorocha ya ce lamarin ya samu nasara ne saboda mutane musamman ‘yan kasuwa ba su san matsala, wannan ya sa suka zauna a gidajen su.

Okorocha ya kira wa’adin da aka baiwa Inyamurai a Arewa a matsayin shiririta da neman tashin hankali.

Ya ce ‘yan kabilar Inyamurai mutane ne da ke son zaman lafiya, wanda kuma ke taka rawa sosai wajen bunkasa tattalin arzikin Nijeriya fiye da kowacce kabila a Nijeriya.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel