Yansanda sun kama ýan luwaɗi da masu fyaɗe sama da 100 a jihar Kano

Yansanda sun kama ýan luwaɗi da masu fyaɗe sama da 100 a jihar Kano

- Yansanda sun kama ýan luwaɗi da masu fyaɗe sama da 100 a jihar Kano

- Yansandan sun kama masu laifin ne a watannin Uku kacal

Jimillan masu fyade da yan luwadi 124 ne rundunar Yansandan jihar Kano ta kama a cikin watanni uku kacal, inji wani rahoton jaridar Daily Trust.

Dayake baje ma manema labaru masu laifin, Kaakakin rundunar Yansandan, DSP Magaji Musa Majia yace an samu ayyukan fyade, luwadi da sauran kazaman ayyuka guda 115 a tsakanin watan AFrilu zuwa Yuni.

KU KARANTA: Tambuwal ya aika Shehunnan Malamai 90 Makkah don yi ma Najeriya addu’a

Majia yace mutane 124 ne suka aikata munanan ayyukan, sa’annan mutane 128 ne aka aikata ayyukan akan su, sun mika kyasakyasai 94 gaban kotu, yayin da suke gudanar da bincike akan guda 13.

Yansanda sun kama ýan luwaɗi da masu fyaɗe sama da 100 a jihar Kano

Yansanda sun kama ýan luwaɗi

Kaakakin ya nuna bacin ransa da karuwar munanan ayyuka a jihar Kano, sai dai ya tabbatar da cewar rundunarsu zata cigaba da aikinta na maganin ire iren su, kamar yadda majiyar NAIJ.com ta ruwaito.

“Kwamishinan yansanda Rabiu Yusuf yayi alkawarin hukumar zata yi amfani da kwarewa a yayin binciken duk wani kes data shafi luwadi da fyade, kuma zamu gurfanar da wanda suka samu da hannu.” Inji DSP Majia.

Daga karshe ya shawarci iyaye dasu lura da irin abokanan yaransu, da wadanda suke mu’amala dasu, sa’annan ya bukaci Malamai da shuwagabannin gargajiya dasu taimaka wajen magance matsalar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ya zakayi idan kaga miliyan 100 a asusun ka?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel