Madalla: Za'a dauki dubban mutane aikin koyarwa a Firamare da Sakandare a wannan jihar ta Arewa

Madalla: Za'a dauki dubban mutane aikin koyarwa a Firamare da Sakandare a wannan jihar ta Arewa

- Gwamnatin jihar Katsina ta sanar da fara tantance mutane 3,000 da suke nemi aikin koyarwa a jihar.

- Shugaban ma’aikatar SUBEB Lawal Buhari a jihar ya sanar da hakan inda ya ce kwamitin tantance ma’aikatan za ta fara ne da tanttance takardun gama makaranta wadanda suka nemi aikin.

Ya baiyana cewa wadanda suka sami nasara a jarabawar daukan malaman da jihar ta gudanar daga masarautar Daura da ya hada da Sandamu, Mai’adua, Baure da Zango sun kai su 722.

NAIJ.com ta samu labarin cewa Buhari ya jinjinawa gwamnan jihar Katsina Aminu Masari kan kokari da yake na ganin ya bunkasa fannin ilimi a jihar ta hanyar gyara ajujuwan makarantu da kuma samar da ababen da makarantan ke bukata.

Madalla: Za'a dauki dubban mutane aikin koyarwa a Firamare da Sakandare a wannan jihar ta Arewa

Madalla: Za'a dauki dubban mutane aikin koyarwa a Firamare da Sakandare a wannan jihar ta Arewa

Daya daga cikin mambobin kwamitin tantancewar kuma kwamishinan matasa da wasani Abdullahi Abu ya ce za su kwatanta yin gaskiya da adalci yayin gudanar da aikin su.

A takaice dai jihar Katsina zata dauki malaman makaranta 1,900 wanda za su yi aiki a makarantu firamare da sakandare a jihar.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duba da sakamakon babban zaben PDP, anya Atiku bai yi kamun gafiyar baidu ba?

Duba da sakamakon babban zaben PDP, anya Atiku bai yi kamun gafiyar baidu ba?

Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi
NAIJ.com
Mailfire view pixel