'Kabilar Ibo na arewa laifinsu daya da na kudu' - Shugaban samarin Arewa

'Kabilar Ibo na arewa laifinsu daya da na kudu' - Shugaban samarin Arewa

- Ana cike da juna tsakanin kabilun kasar nan

- An fasa kama shugaban samarin arewa

- Ana cacar-baka tsakanin kabilun kudu da arewa

A hirar sa da 'yan jarida, shugaban samaron arewa, Shettima Yerima, yace su ba rigima suke so ba, cikin lumana zasu kori kabilar Ibo domin su kafa tasu kasar a kudancin Najeriya. An tambaye shi batun kama shi ko gayyatar hukuma, yace ya zuwa yanzu, babu wanda ya gayyace shi ko ya bashi sammaci.

Da aka tambaye shi batun ko sun dora wa wasu laifin wasu, sai ya kada baki yace, ai laifin na arewa iri daya ne da na kudu, domin su kabilar Ibo na arewar suna ji na kudu na tsangwamar arewa, suna kuma kurarin kafa tasu kasar, amma basu ce uffan ba.

Ya ce: "Kaga kenan zamu dauka duk bakinsu daya, in ba don haka ba, ai sai su fitar da sanarwa su ce su ba su cikin IPOB, ko kuma ba da yawunsu ake yi ba."

Kabilar Ibo na arewa laifinsu daya da na kudu' - Shugaban samarin Arewa

Kabilar Ibo na arewa laifinsu daya da na kudu' - Shugaban samarin Arewa

Da aka tambaye shi ko ta karfi zasu kori kabilun in basu tafi ba sai yace a'a, zasu bi cikin lumana, kuma zasu yi duk yadda zasu yi kar abin ya zarce ikon su, amma suna so hukumomi su san akan dai-dai suke, ba rigima ba.

Ya zuwa yanzu dai, hukumomi sun ce a kai zuciya nesa, kuma an yi kira da duk kabilu su zauna inda suke, su kuma mutunta juna.

Shugaba Osinbajo kuma, yayi kakkausan lafazi kan zasu hukunta suk wanda ke da zimmar ta da zaune tsaye.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel