Shugaban EFCC, Magu ya fada ma gwamnatin Najeriya da ta gina kurkuku matsakaici a Sambisa

Shugaban EFCC, Magu ya fada ma gwamnatin Najeriya da ta gina kurkuku matsakaici a Sambisa

- Shugaban EFCC, Magu ya shawarci gwamnatin Najeriya da ta gina kurkuku matsakaici a Sambisa

- A cewar sa mutane masu aikata rashawa za'a dunga zubawa a wannan kurkuku idan an gina

- Ya ce hakan zai kuntata masu sannan ya raba su da duk wani jin dadinsu

- Ya kuma sha alwashin kawo karshen rashawa a kasar

Mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa wato EFCC, Ibrahim Magu ya yi kira ga gwamnatin tarayyana Najeriya da ta gina matsakaicin kurkuku a dajin Sambisa musamman saboda mutane masu rashawa.

Ya ce dalili rokon shine domin a nuna karara cewa aikata rashawa ba abu bane da za’a yarda da shi a kasar.

KU KARANTA KUMA: EFCC na binciken Yakubu Dogara kan kasafin Najeriya

Da yake magana a lokacin da ya tarbi tawagar masu sadarwa na kungiyar magoya bayan Buhari (NCBSG) a ranar Litinin a ofishin sa dake Abuja, Magu ya ce idan aka amince, zai zamo kurkuku na musamman ga mutane masu aikata rashawa, wanda hakan zai katange su daga jama’a tare da yanke masu jindadin su.

Shugaban EFCC, Magu ya fada ma gwamnatin Najeriya da ta gina kurkuku matsakaici a Sambisa

Shugaban EFCC, Magu ya fada ma gwamnatin Najeriya da ta gina kurkuku matsakaici a Sambisa

Ya yi korafin cewa idan aka ajiye su a kurkukun Kirikiri dake Lagas, “suna ci gaba da harkokin gabansu kamar babu wani abu, suna amfani da na’urar sadarwan su, alhalin, ayyukan su ne ke jefa Najeriya a halin talauci fiye da sauran kasashen duniya. Matsakaicin kurkuku a dajin Sambisa domin mutane masu rashawa”.

Magu ya kara da cewa: “Hukumar EFCC bazata bar wani kafa ba, zamu tabbatar da cewa mun ci gaba da samun matsayi mafi girma a kasar gurin kawo karshen ayyukan rashawa.

Magu ya ce hukumar yaki da rashawa ta ta’allaka ne gurin kawo karshen rashawa a kasar.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

NAIJ.com ta kawo maku bidiyon gangamin hukumar yaki da cin hanci da rashawa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel