EFCC na binciken Yakubu Dogara kan kasafin Najeriya

EFCC na binciken Yakubu Dogara kan kasafin Najeriya

- Hukumar EFCC na bincikar kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara

- Ta na binciken sa ne a kan zargin kara wasu alkaluma a kasafin kudin 2016

Hukumar yaki da cin hanci da hana yi wa tattalin arziki zagon kasa wato EFCC na binciken kakakin Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara a kan zargin sa da kara wasu alkaluma a kasafin kudin shekarar 2016 ba bisa doka ba.

NAIJ.com ta samu labarin cewa wata takardar wasika da aka rubuta a ranar 9 ga watan Yuni, ta nuna cewa Mista Dogara ya kara alkaluman ne bayan Majalisa ta amince da kasafin kudin.

KU KARANTA KUMA: Rundunar ‘Yan sanda za suyi atisayi a Abuja

EFCC na binciken Yakubu Dogara kan kasafin Najeriya

EFCC na binciken Yakubu Dogara kan kasafin Najeriya

Zuwa yanzu dai mai magana da yawun Dogara bai mayar da martani ba dangane da wannan rahoton duk da kiran sa da manema labarai suka yi ta wayar tarho.

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya sha alwashin yakar cin hanci da rashawa da ke ci gaba da haifar da koma-baya ga kasar Najeriya.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

NAIJ.com ta kawo maku bidiyon gangamin hukumar yaki da cin hanci da rashawa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An gudanar da zaben Ekiti cikin gaskiya da aminci – INEC ta maida martani ga PDP

An gudanar da zaben Ekiti cikin gaskiya da aminci – INEC ta maida martani ga PDP

An gudanar da zaben Ekiti cikin gaskiya da aminci – INEC ta maida martani ga PDP
NAIJ.com
Mailfire view pixel