Satar kuɗin gwamnati: Da ƙyar muke iya biyan albashi a baya – Inji Minista

Satar kuɗin gwamnati: Da ƙyar muke iya biyan albashi a baya – Inji Minista

- Amaechi yace a farkon hawan gwamnatin Buhari ko albashi wuyan biya yake yi

- Amaechi yace kalubalen da suke shine magance matsalolin rashin ababen more rayuwa

Tsohon gwamnan jihar Ribas Rotimi Amaechi, kuma ministan harkokin sufuri, ya bayyana cewar a farkon hawan gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ko albashi wuyan biya yake yi, saboda halin da suka tarar da asusun gwamnatin kasar.

Amaechi ya bayyana haka ne a ranar Talata 13 ga watan Yuni, ind yace “Tsabagen tabargazar da muka tarar a gwamnatin baya, albashi ma da kyar muke biya da muka kama madafan iko.”

KU KARANTA: Solomon Dalung ya ziyarci Shehi Dahiru Bauchi a gidansa (HOTUNA)

Premium Times ta ruwaito Amaechi yana fadin babban kalubalen dake fuskantar gwamnatin APC shine magance matsalolin rashin ababen more rayuwa, kuma gwamnati ta dage tukuru ganin cewa ta inganta rayuwar yan Najeriya, inji shi.

Satar kuɗin gwamnati: Da ƙyar muke iya biyan albashi a baya – Inji Minista

Amaechi da Jonathan

Dayake bayani akan matsayin kafafen sadarwa na zamani a siyasa, Amaechi yace kafafen na samar da ayyukan yi ga matasa, amma kuma suna da irin nasu matsalar, don haka ne ya shawarci matasa dasu dinga amfani da kafafen sadarwa ta yadda ya dace.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

NAIJ.com ta kawo muku bidiyon jimamin mutuwar Keshi.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
PDP ta azabtar da kudancin yamma saboda sun sabi Buhari a 2015

PDP ta azabtar da kudancin yamma saboda sun sabi Buhari a 2015

PDP ta azabtar da kudancin yamma saboda sun sabi Buhari a 2015
NAIJ.com
Mailfire view pixel