Biyafara: Jonathan ne ya yaudari Inyamurai – Inji Amaechi

Biyafara: Jonathan ne ya yaudari Inyamurai – Inji Amaechi

- Amechi yace Jonathan ya watsa ma Inyamurai ƙasa a idanu

- Amaechi abinda Buhari keyi ma Inyamurai yafi wanda Jonatha yayi

Ministan harkokin sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana cewar duk da irin goyon bayan da Inyamurai suka baiwa tsohon shugaban kasa Jonathan, amma basu ci moriyarsa ba.

Amaechi ya bayyana haka ne a ranar Talata 13 ga watan Mayu a jihar Legs yayin dayake gabatar da kasida akan muhimmancin kafafen sadarwa na zamani a siyasan Najeriya, inji rahoton Premium Times.

KU KARANTA: Osinbajo ga ýan Majalisu: Baku da ikon yin ƙare ƙare a kasafin kuɗi

“Inyamurai sun goya Jonathan, amma me yayi musu? Jonatha yaje garin Onitsha yayi alkawarin gina babbar gadar Onitsha, amma daga bisani me ya faru? Amma sai gashi a yau muna gudanar da aikin gyaran gadan Onitsha, tare da gina sabon gada.” Inji Amaechi.

Biyafara: Jonathan ne ya yaudari Inyamurai – Inji Amaechi

Jonathan

Amaechi ya soki shuwagabannin PDP na yankin kudu maso gabas, day ace duk da suna da daman ganin Jonathan, amma basu neman ma al’ummarsu komai ba, sai dais u neman ma aljihunansu.

“Cikin ikon Allah, sai ga shi Buhari na sabunta gina hanyar Fatakwal zuwa Owerri, sa’annan muna yin Fatakwal zuwa Enugu, sa’annan muna yin Fatakwal zuwa Onitsha, kuma nan bada dadewa ba zamu diran ma titin Enugu zuwa Onitsha.” Inji Amaechi

Dayake jawabi akan ko shugaba Buhari zai iya samun kuri’un mutanen yankin ARewa maso gabas, majiyar NAIJ.com ta ruwaito Amaechi yace mutanen yankin sun gode da kokarin da Buhari yayi musu na tseratar dasu daga sharrin Boko Haram.

Daga karshe yace, yawan kuri’un da za’a samu a 2019 daga yankin ARewa maso gaba sai sun ninka na 2015.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Zaman lafiya a Najeriya, Osinbajo yayi batu:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel