Dalar Amurka na cigaba da yin kasa a kasuwar canji

Dalar Amurka na cigaba da yin kasa a kasuwar canji

– A halin yanzu darajar Dala na cigaba da yin kasa a kasuwar canji

– Babban bankin kasar na cigaba da sakin daloli a kasuwa

– Yanzu dai an kara sakin wasu Dala Miliyan 400 a kasuwa

Babban bankin Najeriya CBN na cigaba da aman Daloli. Hakan ya sa Dalar ke kara sauka kasa inda Naira ke tashi. Cikin makon nan dai CBN ya saki makudan Miliyoyin daloli.

Dalar Amurka na cigaba da yin kasa a kasuwar canji

Dalar Amurka na rage daraja a Najeriya

Babban bankin Najeriya na CBN na cigaba da sakin makudan miliyoyin daloli a kasuwar canji babu kama hannun yaro. A Ranar Litinin dai Gwamnan CBN ya saki Dala Miliyan 413.5 domin ‘yan canji wanda hakan ya sa Naira ta kara mikewa yayin da Dalar ke kara sauki.

KU KARANTA: Dan wasan kwallo Ronaldo bai biyan haraji?

Dalar Amurka na cigaba da yin kasa a kasuwar canji

CBN na ta sakin makudan Miliyoyin daloli

Gwamnan CBN ya saki kusan Dala Miliyan 50 domin ‘yan kasuwa da kuma wasu Dala Miliyan 42 ga masu bukatar fita kasashen waje. Mun samu labari cewa har Dalar ta fara yin kasa da N360 a hannun ‘yan canji.

Kwanaki Mai kudin Afrika Alhaji Aliko Dangote yace Gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele yayi kokarin wajen fitar da Najeriya daga kangin da aka shiga na tattalin arziki. Yanzu dai Najeriya na shirin fita daga matsin tattalin arziki.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ko Jama'a na kewar Shugaban kasa Buhari?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiya ta bukaci Buhari ya yiwa gwamnatocin bayan sa binciken kwa-kwaf

Kungiya ta bukaci Buhari ya yiwa gwamnatocin bayan sa binciken kwa-kwaf

Kungiya ta bukaci Buhari ya yiwa gwamnatocin bayan sa binciken kwa-kwaf
NAIJ.com
Mailfire view pixel