Za a iya jefa Dan wasa Cristiano Ronaldo a gidan yari

Za a iya jefa Dan wasa Cristiano Ronaldo a gidan yari

– Ana zargin Dan wasan Duniya Ronaldo da laifin rashin biyan haraji

– Hukuma za ta tuhumi ‘Dan wasan da wannan babban laifi

– Akwai yiwuwar Dan wasan bai biya sama da Dala Miliyan 16 na haraji ba

Ana iya kama babban Dan wasa Ronaldo da laifin haraji. Haka dai aka yi da Dan wasa Lionel Messi. Duk Duniya babu Dan kwallon da ya kai sa karbar albashi.

Za a iya jefa Dan wasa Cristiano Ronaldo a gidan yari

Dan wasan Duniya Cristiano Ronaldo da 'Yan uwan sa

Ana zargin Babban Dan wasan kwallon kafar nan na Duniya Cristiano Ronaldo da rashin biyan kudin harajin da ke kan sa na sama da Dala Miliyan 16. Kwanaki Kotu ta yankewa Lionel Messi daurin watanni 21 bayan an same sa da irin wannan laifi na kin biyan haraji.

KU KARANTA: Dan wasa Ronaldo ya samu 'yan biyu

Za a iya jefa Dan wasa Cristiano Ronaldo a gidan yari

Ana zargin Dan wasa Ronaldo da laifin haraji

Akwai zargin cewa Dan wasan bai bayyana asalin abin da yake samu ba wanda ta hakan ne ya biya kasa da abin da ya kamata ya ba Hukuma a matsayin kason haraji. Ronaldo dai na samun kudi ta wasu hanyoyin iri-iri ban da albashin sa irin su talla da kudin rigar wasa.

A jerin ‘Yan wasan kwallon da su ka fi kowa albashi a Duniya Cristiano Ronaldo ne kan gaba inda a bana kurum ya tashi da sama da Dala Miliyan 88 sannan Dan wasa Lionel Messi na Barcelona ya hada Dala Miliyan 81 a wannan shekara.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko http://twitter.com/naijcomhausa

Charley Boy ya jagoranci zanga-zanga a Legas

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel