An baiwa El-Rufai wa'adin sati uku shima a Kaduna

An baiwa El-Rufai wa'adin sati uku shima a Kaduna

- A Kaduna, an rufe makarantun kudancin Kaduna tsawon watanni

- Wasu dalibai sun baiwa gwamnati sati uku ta bude makarantun ko taga abun da suke niyyar yi

- A Kaduna dai ana samun sabani tsakanin kabilu da addinai a lokuta da dama

A taro da manema labarai da suka yi, kungiyar samarin kudancin kaduna ta Southern Kaduna Youth Forum, ta fitar da sanarwar baiwa gwamna wa'adin sati uku ko ya fitar musu da jaddawalin sake komawa makaranta ko kuma ya fuskanci hushinsu.

A cewar wata Sanarwar ta bakin Ezekiel David, sakataren kungiyar ya bayyana cewa: "Albarkacin watan Ramadana, mun dauki aniyar kwato wa mutanen yankin mu darajar su don haka mun yanke wa gwamna El-Rufai sati uku ko ya bude mana makaranta mu dena zaman banza, ko ya fuskanci fushin mu.

"Abin mamaki sai ace wadanda suke cewa su ne masu kishin ilmi a kasa amma sun ware wani bangare na al'ummarsu, sun hana su ilmin. Banda Malam Nasir El-Rufai, babu wanda ya san wannan dalili."

An baiwa El-Rufai wa'adin sati uku shima a Kaduna

An baiwa El-Rufai wa'adin sati uku shima a Kaduna

Kwamared Galadima Jesse, Shugaban kungiyar ya bayyana cewa an rufe makarantun Noma na jami'ar Kasu da ke yankin, an kuma rufe kwalejin koyan ilimin jinya da kwalejin ilimi a kafanchan, tun lokacin rikicin kabilanci a bara. Kuma babu ranar budewa.

A cewar gwamnati dai, rikicin kabilanci ne ya jawo aka rufe wasu makarantun. An bude wasu makarantun, wasu kuwa har yanzu a rufe suke.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel