Osinbajo ga ýan Majalisu: Baku da ikon yin ƙare ƙare a kasafin kuɗi

Osinbajo ga ýan Majalisu: Baku da ikon yin ƙare ƙare a kasafin kuɗi

- Farfesa Yemi Osinbajo ya soki lamirin majalisa

- Osinbajo ya nuna bacin ransa da yadda majalisa ta bata lokaci a kasafin kudin

Mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewar majalisa bata da ikon kare kare a cikin kasafin kudi, ko su sauya wani abu daga cikinsa , inji rahoton Daily Trust.

Osinbajo ya bayyana haka ne a fadar shugaban kasa yayin kaddamar da shirin aikin kasafin kudin bana, inda ya nuna bacin ransa ta yadda majalisa ta bata lokaci wajen kammala tantance kasafin kudin

KU KARANTA: YANZU YANZU: Osinbajo ya sanya baki a kan wa’adin barin gari da aka gindaya ma ‘yan kabilar Igbo

“Na tabbata yanzu mun san yadda zamu gyara matsalolin da muka tarar, misali tun a watan Disambar bara shugaban kasa ya mika ma majalisa kasafin kudin, amma basu kammala aiki akansa ba sai a Mayu, gaskiya bamu ji dadin yadda ya dade a hannunsu ba.

Osinbajo ga ýan Majalisu: Baku da ikon yin ƙare ƙare a kasafin kuɗi

Osinbajo yayin dayake rattafa hannu a kasafin kuɗi

“Kuma bai kamata ace sun kaar sabbin ayyuka a cikin kasafin kudin ba, ko kuma a canza mana ayyukan da muka gabatar muke son yi.” Inji Osinbajo.

Daga karshe, Farfesa Osinbajo ya bada tabbacin zuwa watan Oktoba zasu mika ma majalisa kasafin kudin na badi, kamar yadda majiyar NAIJ.com ta ruwaito.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Zancen Osinbajo akan Biafar

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel