Manjo Al-Mustapha ya roki El-Rufai da ya janye sa wa da ya yi a kama shugabannin kungiyoyin Matasan Arewa

Manjo Al-Mustapha ya roki El-Rufai da ya janye sa wa da ya yi a kama shugabannin kungiyoyin Matasan Arewa

- Manjo Hamza Al-mustapha ya bukaci gwamnan jihar Kaduna mallam Nasir El-Rufai da ya mai da takobin sa a kan kungiyoyin matasan Arewa da ya sa a kama

- Ya yi kira ga matasa da su dunga tauna magana kafin su fitar da ita

- Shugaban kungiyar MASSOB Ralph Nwazurike ya ce kungiyarsa babu ruwa ta da Nnamdi Kanu

Tsohon Shugaban mai ba tsohon shugaban kasa Janar Sani Abacha tsaro Manjo Hamza Al-mustapha ya bukaci gwamnan jihar Kaduna mallam Nasir El-Rufai da ya mai da takobin sa, cewa ya janye daga sa wa da ya yi a kama shugabannin kungiyoyin Matasan Arewa da suka ba ‘yan kabilar Igbo wa’adin watanni uku su tattara inasu-inasu su koma yankin su.

Al-Mustapha ya fadi haka ne a lokacin da ya jagoranci shugaban kungiyar MASSOB Ralph Uwazurike zuwa jihar Kaduna domin neman sulhu da kungiyoyin matasan Arewan.

Al-Mustapha ya yi kira ga matasan da su dunga tauna magana kafin su furta saboda kada ya jawo irin wannan cece-kuce ko kuma ta da hankalin ‘yan Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Bai kamata shugaban kasa ya nada shugaban hukumar zabe ba - Jega

Manjo Al-Mustapha ya roki El-Rufai da ya janye sa wa da ya yi a kama shugabannin kungiyoyin Matasan Arewa

Manjo Al-Mustapha ya roki El-Rufai da ya janye sa wa da ya yi a kama shugabannin kungiyoyin Matasan Arewa

Ana shi jawabin shugaban kungiyar MASSOB Ralph Nwazurike ya ce kungiyarsa babu ruwa ta da Nnamdi Kanu wanda ke fafutukar kafa kasar Biyafara domin shine ya kafa gidan Rediyon Biafra sannan ya nada shi shugabancinta amma kafin ya ankara ‘yan siyasar kabilar Igbo din su kayi kaca-kaca da manufar kafa wannan gidan Radiyo.

Ya ce ya na yi masu alkawarin cewa za su kare mutunci da lafiyar duk wani dan Arewa da ke yankin Kudu Maso Gabashin Najeriya.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel