Hukumar FRSC zata fara gwajin ciwon hauka akan direbobi

Hukumar FRSC zata fara gwajin ciwon hauka akan direbobi

- FRSC zata fara gudanar da gwajin tabin hankali akan masu karya dokokin tuki

- Shugaban hukumar FRSC, Boboye Oyeyemi ya bayyana haka ne

Daga ranar 1 ga watan Yulio ne hukumar kare haddura ta kasa, FRSC zata fara gudanar da gwajin tabin hankali akan masu karya dokokin tuki, musamman masu amsa waya suna tuki.

Shugaban hukumar FRSC, Boboye Oyeyemi ya bayyana haka ne a ranar Litinin 12 ga watan Yuni yayin gudanar da taron kara ma juna sani akan jami’an hukumar a garin Abuja.

KU KARANTA: Sojoji sun gudanar da aikin gayya a jihar Legas (Hotuna)

Oyeyemi yace doka ta basu daman gudanar da wannan gwajin tabin hankali akn direbobi masu yawna karya dokokin tuki, kamar yadda majiyar NAIJ.com, Daily Post ta ruwaito.

Hukumar FRSC zata fara gwajin ciwon hauka akan direbobi

Hukumar FRSC

“Yawaitan samun direbobi masu amsa waya akan manyan hanyoyi yayin da suke tuki na damun mu. Don haka muka gayyaci manyan jami’an mu domin horar dasu akan yadda zasu gudanar da gwajin hauka akan direbobin da kuma asibitocin da zasu kai su.

“ A gani na rashin hankali ne na karshe ace mutum yana amsa waya yayin dayake tuki. Hakan na nuna cewa irin wannan mutumi yana da tabin hankali, don haka lallai ne a duba shi.” Inji shi

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wa yafi karya, mace ko namji?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu, Inji Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu, Inji Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC
NAIJ.com
Mailfire view pixel