Duk wanda yake kiran masifa bai santa ba ne – Inji gwamnan Borno

Duk wanda yake kiran masifa bai santa ba ne – Inji gwamnan Borno

- Gwamnan jihar Borno Kashim Shetima ya ce duk wanda yake kiran masifa ko yaki tabas bai santa ba ne

- Shattima y ace duk wanda ya san yaki ba zai yi irin kalamun da matasan arewa suka yi ba na cewa kabilar Igbo su bar jihohin arewa

- Gwamnan ya ci gaba da cewa idan matasan arewa basu san ma'anar rashin zaman lafiya ba su nemi wani a jihar Borno yayi masu bayani

A matsayinsa na shuagaban kungiyyar gwamnonnin Arewa 19 ya ce yana ganin wadanda suka ba mutane wa'adin ficewa daga kasarmu suna neman su tada fitina basu san yaki ba ne idan ba haka ba matasan arewa ba zasu yi furucin da suka yi ba

Akan fadin ra'ayi gwamnan Borno Kashim Shetima yace akwai banbanci da kokarin tada fitina kamar yadda matasan Arewa suke neman yi da bayyana ra'ayi.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, gwamnan ya cigaba da cewa duk wanda yake neman tada zaune tsaye bai san tashin hankali ko yaki ba ne. Yana mai cewa duk wanda ya san yaki ba zai yi irin kalamun da matasan arewa suka yi ba na cewa kabilar Igbo su bar jihohin arewa nan da watanni uku.

Duk wanda yake kiran masifa bai santa ba ne – Inji gwamnan Borno

Gwamnan jihar Borno Kashim Shetima

KU KARANTA: ‘Yan sanda sun ba ‘yan kabilar Igbo mazauna Kano tabbacin samun kariya da ya dace

A cewar gwamna Shettima yau idan akwai wanda ya fi kowa sanin masifar dake tattare da rashin zaman lafiya shi ya fi kowa sani a matsayinsa na kasancewa gwamnan jihar Borno mahaifar 'yan ta'addanci Boko Haram. Yace idan yaro yace bai iya gudu ba bai ga abun gudu ba ne. Yace idan matasan arewa basu san ma'anar rashin zaman lafiya ba su nemi wani a jihar Borno yayi masu bayani.

Yace a matsayinsu na kasancewa shugabannin a arewa idan sun ga abun da zai kawo tashin hankali da rashin zaman lafiya dole ne su tsawata saboda banbancinsu ke nan da sauran kasar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon rikicin kudancin jihar Kaduna kashi na 2

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel