Korar kabilar Ibo: 'Sai mun kone duk dukiyarmu zamu bar arewa'

Korar kabilar Ibo: 'Sai mun kone duk dukiyarmu zamu bar arewa'

- An shawarci kabilar Ibo da su kwashe arzikinsu in har ta tabbata korar su za ayi

- An basu shawara su kone abun da ba zai dauku ba

- An ji tsit, batun kame samarin arewa da suka yi wa kabilu barazana

Cif Nathaniel Amaechi, shugaban kabilar Ibo mazauna jihar Ekiti, ya yi tir da kiraye-kiraye da ake wa juna tsakanin kabilun kasar nan, inda yace wannan wani abun kunya ne, musamman ganin ba'a kama kowa ba a lamarin.

Cif Amaechin, yana magana ne kan batun wai wa'adin korar kabilar Ibo daga arewa, inda yace yayi mamaki manyan arewa da manyan kasarnan basu furta komai kan batun ba, ba kuma su nuna ko-in-kula ba.

Yace mutane irin su shugaba Obasanjo, IBB da ma gwamnatin tarayya basu ce uffan ba ko tir da batun, wannan abin takaici ne, a cewarsa.

Korar kabilar Ibo: 'Sai mun kone duk dukiyarmu zamu bar arewa'

Korar kabilar Ibo: 'Sai mun kone duk dukiyarmu zamu bar arewa'

Ya kuma yi kira ga kabilar Ibo da su yi zamansu a inda duk suke ba tare da tsangwama ba, ya kuma ce lallai a zauna lafiya, amma idan aka ce wa'adin da gaske ne, to "kabilar Ibo su sayar da duk dukiyoyinsu, su kuma kone sauran da baza su iya diba ba, su mayar da arewar hamada, kamar yadda suka same ta."

A cewarsa, muddin hakan ya auku, kabilar Ibo ita ce zasu yi nasara, inda yace arewar ce zata yi asara mai yawa, saboda dumbin dukiya da kadarori na tiriliyoyin nairori da suka zuba jari a arewar.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras

NAIJ.com
Mailfire view pixel