An ɗaure shi saboda ya busa sigari a watan Ramadana

An ɗaure shi saboda ya busa sigari a watan Ramadana

- Alkali ya yanke ma matashi hukuncin zaman gidan kaso saboda sha sigari

- Matashin ya busa sigari ne a gaban kotu a kasar Tunisia

Wata kotun kasar Tunisia ta aika da wani matashi gidan kasa sakamakon kama shi da tayi da laifin shan sigari a bainar jama’a a yayin gabatar da Azumin watan Ramadana.

Jaridar Punch ne ta dauko rahoton inda tace an kama mutumin ne yana shan sigari a wajen Kotu, inda nan da nan aka sanar da Yansanda suka yi awon gaba da shi, kuma ba tare da bata lokaci ba suka mika shi gaba alkali.

KU KARANTA: Harin ýan bindiga: Sanata ya tsallake rijiya da baya

Sai dai kotu ta baiwa mutumin daman daukaka kara a kwanaki 10. Ko a ranar 1 ga watan Yuni sai da aka daure mutane hudu zuwa zaman watan guda a gidan yari sakamakon cin abinci a bainar jama’a, kamar yadda majiyar NAIJ.com ta ruwaito

An ɗaure shi saboda ya busa sigari a watan Ramadana

An ɗaure shi saboda ya busa sigari a watan Ramadana

Wannan hukuncin kotu ya biyo bayan wani gangamin zanga zanga da wasu mutanen kasar suka gudanar a ranar Lahadi 11 ga watan Yuni domin neman a basu daman su ci abinci a bainar jama’a a watan Ramadana.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Halin da yan Arewa suke ciki a Abuja

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel