YANZU YANZU: Osinbajo ya sanya baki a kan wa’adin barin gari da aka gindaya ma ‘yan kabilar Igbo

YANZU YANZU: Osinbajo ya sanya baki a kan wa’adin barin gari da aka gindaya ma ‘yan kabilar Igbo

- Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo, na shirin ganawa da shugabanni arewa da na yankin kudancin Najeriya

- Osinbajo ya ba shugabannin umurnin kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya a ko ina

Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo, na shirin ganawa da shugabanni daga arewa da yankin kudancin Najeriya don kawo karshen rikicin da ya billo bayan wa’adin barin gari da aka ba ‘yan kabilar Igbo dake daune a yankin Arewa.

NAIJ.com ta samu labarin cewa mataimakin mukaddashin shugaban kasa a shafukan zumunta, Laolu Akande, wanda ya bayyana hakan ta shafin san a Twitter ya ce Osinbajo zai fara ganawa da kungiyoyin a lokuta daban daban kafin ya gana da su a hade.

KU KARANTA KUMA: Bai kamata shugaban kasa ya nada shugaban hukumar zabe ba - Jega

Laolu Akande ya ce mukaddashin shugaban kasar ya fara ganawa da shugabannin hukumomin tsaroa karshen mako, inda a nan ya basu umurnin kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya a ko ina.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

NAIJ.com ta kawo maku bidiyon Osinbajo da yake magana a kan Biyafara

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel